Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan matafiya a jihar Zamfara. Tsagerun sun sace fasinjoji tare da kashe direban motar.
Tsohon shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf ya yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wankin babban bargo.
Tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Government Ekpemupolo, ya bayyana shirin Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike kan Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers.
Tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Government Tompolo, ya roki 'yan Arewa da su goyi bayan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Kungiyar matasan Yarabawa (YYC), ta bi sahun masu kiran da a sanya dokar ta baci a jihar Zamfara. Sun ce hakan zai sanya a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a Borno. Tsagerun sun hallaka mutane 12 ciki har da jami'an tsaro na 'yan sa-kai bayan sun yi musu kwanton bauna.
Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya bayyana cewa PDP za ta ci gajiya sauyar shekar da ake yi zuwa APC a nan gaba.
Kungiyar 'yan majalisar tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Rivers, sun nuna gamsuuwarsu kan kamun ludayin Shugaba Bola Tinubu. Za su mara masa baya a 2027.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa dole sai an hada da dukkanin masu ruwa da tsaki kafin a samu zaman lafiya a jihar Rivers.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari