Hajjin Bana: An Sanya Lokacin Fara Jigilar Alhazai zuwa Saudiyya a Jihar Kwara

Hajjin Bana: An Sanya Lokacin Fara Jigilar Alhazai zuwa Saudiyya a Jihar Kwara

  • Hukumar kula da alhazai ta Kwara ta ce za a fara jigilar alhazan jihar daga birnin Ilorin zuwa kasar Saudiyya a ranar 12 ga Mayu, 2025
  • Sghugaban hukumar ya ce za a yi jigilar rukuni na biyu a ranar 14 ga Mayu, na uku a ranar 16 ga Mayu, sannan na ƙarshe 17 ga Mayu
  • Gwamnatin Kwara ta bukaci alhazan jihar su kasance jakadu na gari a Saudiyya, su nuna ladabi da tsoron Allah yayin aikin Hajjin bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Hukumar kula da alhazai ta Kwara ta sanar cewa za a fara jigilar alhazan jihar daga filin jirgin sama na Ilorin zuwa Saudiyya ranar 12 ga Mayu.

Shugaban hukumar, Abdulsalam Abdulkadir, ne ya bayyana hakan yayin taron wayar da kan alhazai na shekarar 2025 da aka gudanar a Ilorin ranar Lahadi.

Hukumar Alhazan Kwara za ta fara jigilar maniyyaran jihar daga ranar 12 ga Mayu a Ilorin.
Manniyyata aikin Hajji a lokacin da suke shiga jirgi domin jigilarsu zuwa Saudiyya. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Twitter

An sanya ranar fara jigilar Alhazan Kwara

Abdulsalam ya bayyana cewa rukuni na biyu za su tashi ranar 14 ga Mayu, rukuni na uku ranar 16 ga Mayu, sannan na karshe za su tashi ranar 17 ga Mayu, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an riga an tanadi masauki da abinci ga alhazan Kwara daga isarsu har zuwa lokacin kammala aikin Hajji a Saudiyya.

Shugaban hukumar ya kuma tabbatar da cewa shirye-shirye na tafiya daidai, inda za a fara yin alluran rigakafi daga ranar 28 ga Afrilu, a raba tufafi ranar 30 ga Afrilu, sannan jakunkuna ranar 1 ga Mayu.

Abdulsalam ya kara da cewa za a mayarwa alhazan da suka biya fiye da Naira miliyan 8.4 kudin da suka haura wanda aka kayyade bayan sun dawo daga Saudiyya.

An koyar da alhazan Kwara aikin Hajji

A cewar hukumar kula da alhazan:

"Shirye-shiryen hukumar don gudanar da aikin hajjin 2025 sun kusa kammaluwa, kuma an riga an kammala aikin bizar dukkanin alhazai 2,174."

Alkalin kotun shari'ar Musulunci ta jihar Kwara, Mai shari'a Abdul-Lateef Kamaldeen, ya wayar da kan alhazan kan yadda ake gudanar da ibadun Hajji da abin da ake sa ran su aikata.

Mai shari'a Abdul-Lateef ya bukaci maniyyatan da su gudanar da aikin Hajj bisa ladubban da aka koyar, su kuma sanya hakuri da tsoron Allah domin yin ibada karbabbiya.

Taron wayar da kan maniyyatan na kwanaki biyu, ya samu halartar manyan jami'ai da dama, ciki har da tsohon shugaban hukumar, Alhaji Mohammed Tunde-Jimoh.

An shawarci maniyyata Hajji a Kwara da su zamo jakadu na gari a kasar Saudiyya
Maniyyatan Najeriya a lokacin da suke hawa jirgi domin jigilarsu zuwa kasar Saudiyya. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Facebook

Gwamnatin Kwara ta gargadi maniyyatan jihar

Gwamnatin Kwara ta bukaci alhazan jihar da su zama jakadu na gari, ta hanyar nuna jajircewa da mayar da hankali a lokacin aikin Hajjin 2025 a Saudiyya, inji rahoton Radio Nigeria.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Mamman Saba Jibril, ne ya yi wannan kiran yayin jawabin da ya gabatar a wajen taron wayar da kai da addu'a da hukumar kula da alhazai ta shirya a Ilorin.

Farfesa Jibril, wanda babban sakataren sashen kula da ayyuka, Alhaji Abdulganiyu Shuaib, ya wakilta, ya karfafa gwiwar alhazan da su nuna hali nagari a ƙasa mai tsarki.

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar alhazai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shirye-shiryen jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki domin aikin Hajjin bana na ci gaba da samun nasara.

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa ana sa ran fara jigilar maniyyata zuwa Saudiyya cikin watan Mayu, 2025.

Daraktan ayyuka na NAHCON ya bayyana cewa ana sa ran Saudiyya za ta bude sararin samaniyarta a karshen watan Afrilu, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.