'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ramuwar Gayya a Zamfara, an Yi Gagarumar Barna

'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ramuwar Gayya a Zamfara, an Yi Gagarumar Barna

  • Ƴan bindiga sun kai hari ramuwar gayya a ƙauyen Tashar Sahabi da ke ƙaramar hujumar Maru ta jihar Zamfara
  • Miyagun sun kai harin ne bayan ƴan sa-kai sun samu gagarumar nasara a kansu yayin wani artabu da suka yi
  • A yayin harin na ƴan bindiga, an ji cewa miyagun sun ƙona shaguna tare da yin awon gaba da dabbobi masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun ƙaddamar da sabon hari na ramuwar gayya a wani ƙauyen jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun ƙona shaguna tare da sace dabbobi a ƙauyen Yar Tashar Sahabi da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce harin da ƴan bindigan suka kai da sanyin safiyar ranar Talata, wata ramuwar gayya ce kan kisan da ƴan sa-kai suka yi wa wasu daga cikinsu a baya-bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyagun Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Zamfara

A cewar mazauna yankin, ƴan sa-kai sun kai samame a ranar Lahadi, suka kashe ƴan bindiga da dama tare da kwato dabbobin da suka sace.

“Sun zo da asuba, suka bankawa shagunanmu da motoci wuta, sannan suka tafi da dabbobinmu."

- Wani mazaunin yankin

Sai dai jami’an tsaro da ke zaune a kusa da Magami sun gaggauta mayar da martani, inda suka fatattaki ƴan bindigan kafin su ci gaba da ɓarna.

Ƴan bindiga na kai hare-haren ramuwar gayya

Wannan hari na cikin jerin hare-haren ramuwar gayya da ƙungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa a jihar.

A ƙaramar hukumar Tsafe, ƙauyuka da dama sun fuskanci hare-hare waɗanda mutane ke bayyanawa a matsayin na ramuwar gayya.

Tun da farkon wannan wata, ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Keta bayan an kashe wani babban hatsabibin ɗan bindiga da aka fi sani da suna Dan Isuhu.

A lokacin harin, an kashe mutum guda, an ƙona motoci 11, kuma an fasa shaguna tare da sace kayayyaki.

A wannan rana kuma, wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Gidan Arne inda suka harbe mutane uku sannan suka yi garkuwa da mata sama da 40.

Mutum biyu daga cikin waɗanda aka harba sun mutu nan take, yayin da mutum na uku aka garzaya da shi zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba.

'Yan sanda
'Yan bindiga sun kai harin ta'addanci a Zamfara Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jiihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce bai da masaniya kan harin da aka kai a ƙauyen Yar Tashar Sahabi.

Sai dai ya yi alƙawarin kiran DPO na Maru don samun ƙarin bayani, inda ya ce a ɗan saurare shi kaɗan.

"Bari na kira DPO na Maru don samun ƙarin bayani."

- DSP Yazid Abubakar

Sai dai, kakakin ƴan sandan bai sake kira ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun hallaka limami

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka wani limami da suka yi garkuwa da shi a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun hallaka limamin ne kimamin watanni biyu da suka yi garkuwa da shi tare da wasu ƴan uwansa guda biyu.

Kisan mutanen da ƴan bindigan suka yi ya ƙara tada hankulan mutane a jihar Zamfara wacce miyagu suka addaba da hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng