Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnan Jihar Neja da Mataimakinsa, An Ji Abin da Ya Faru
- Rikici ya tsananta tsakanin Gwamna Umaru Bago da mataimakinsa Yakubu Garba, yayin da ake rade-radin cewa zai ajiye aikinsa
- Wasu majiyoyi sun ce wata magana da Yakubu ya yi kuma aka nada aka turawa Gwamna Bago ce ta haddasa wannan sabani a tsakaninsu
- An ce rikicin ya kara kamari ne da Gwamna Bago ya daina mika mulkin jihar ga Yakubu idan zai fita waje, ko tura shi wakilci a manyan taro
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Niger – Rikici tsakanin gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Yakubu Garba, ya ɗauki sabon salo bayan rade-radin cewa Yakubu na shirin murabus.
An ce Yakubu ya fice daga gidan gwamnati da yake zaune da ke gaban cibiyar taro ta Justice Legbo Kutigi, abin da ya ƙara zafafa jita-jitar sabani tsakaninsu.

Asali: Twitter
Sabani tsakanin gwamnan Neja da mataimakinsa
Majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa rikici tsakanin Bago da Yakubu ya fara ne tun bayan da suka kama aiki a watan Mayun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu na danganta rikicin da wata maganar mataimakin gwamnan da aka ce an nada, lokacin da yake korafi game da ayyukan gwamna, sannan aka tura wa gwamnan wannan sauti.
Majiyoyi sun kara da cewa wasu manya daga shiyyar Neja ta Gabas, inda mataimakin gwamnan ya fito, sun hada kai da gwamna don rage karfin Yakubu kafin 2031, lokacin da ake sa ran mulki zai koma shiyyarsu.
An kuma gano cewa ana shirin sauya Yakubu Garba da wani sabon mataimaki a shekarar 2027 da ake ganin Gwamna Bago zai nemi tazarce.
Neja: Wasu dalilai na rikicin Bago da Yakubu
Wani babban zargi da ke ƙara fito da sabanin shi ne cewa Bago ba ya mika wa Yakubu ikon shugabanci idan zai je ƙasar waje, kuma bai fiya tura shi wakilcu a manyan taruka ba.
Sai dai a watan Nuwamba 2024 ne kawai aka ba mataimakin damar rike jihar, lokacin da Gwamna Bago ya tafi hutunsa a Amurka. Haka zalika, ya wakilce shi a taron majalisar zartarwa ta ƙasa a makon da ya gabata.
Wata majiya ta ce abin da ya ƙara zafafa lamarin shi ne wani gargadi da gwamnan ya yi wa mataimakin nasa, inda ya ce ya ja kunnen magoya bayansa.
Majiyar ta ce:
“Gwamnan ya kira mataimakin ya gaya masa cewa ya samu labarin cewa mutanensa na korafi kan 'yan takarar da ake son tsayarwa, ya kuma ce ya shiga taitayinsa. Wannan ne ya sa ya yanke shawarar barin gidan gwamnati."
Ana zargin mataimakin gwamna zai yi murabus
Wani babban jigo a bangaren Gwamna Bago ya tabbatar da niyyar mataimakin gwamna na ajiye aiki.
Jigon ya shaida cewa:
“Gaskiya ne yana shirin barin aiki. Kuma gaskiya ne ya fara kwashe kayayyakinsa daga gidan gwamnati da ofis.
"Amma yana jiran dawowar gwamna daga Rasha kafin ya mikawa majalisa takardar murabus dinsa. Muna kokarin shawo kansa ne kada ya yi hakan."
Ya kara da cewa:
“Kafin zaɓe suna da kyakkyawar alaka. Amma kwatsam sai alakarsu ta yi tsami bayan wasu mutane sun shiga tsakaninsu. Yanzu sun koma ba sa ga maciji da juna.”

Asali: Twitter
Ofishin gwamna da mataimaki sun yi martani
Sai dai a martaninsa, sakataren yada labarai na Gwamna Bago, Bologi Ibrahim, ya ce bai san da wata matsala tsakanin gwamnan da mataimakinsa ba.
“A gaskiya, ba ni da wata masaniya kan wata matsala a tsakanin gwamna da mataimakinsa,” inji Bologi.
Haka zalika, mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Unmulkhatumi Abdullahi Kuta, ta karyata rade-radin cewa Yakubu Garba na shirin murabus, kamar yadda muka ruwaito.
“Tunanin murabus ba ya cikin lissafin mataimakin gwamna. Yanzu haka muna cikin gidan gwamnati tare da shi, kuma babu wani shiri na barin aiki."
- Unmulkhatumi Abdullahi Kuta.
Garba ya magantu kan 'yan gudun hijiran Neja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mataimakin gwamnan Neja, Yakubu Garba ya ce akwai mutane sama da 5,000 da ke gudun hijira a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyara ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ke Abuja.
Yakubu ya shaidawa shugaban hukumar ta NEMA cewa hare-haren 'yan ta'addan da ake yawan samu a jihar ne ya jawo ƙaruwar 'yan gudun hijirar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng