Ministar Abuja Ta Gina Katafaren Masallaci a Kano, Ganduje Ya Yi Maganganu kan Mariya
- Dr. Abdullahi Ganduje ya kai ziyara Kano domin kaddamar da masallacin Juma’a da Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta gina a garinta na haihuwa
- Fitattun jiga-jigan APC sun halarci taron, ciki har da Dr. Nasiru Gawuna, Murtala Sule Garo, Kawu Sumaila da Abdullahi Abbas na jam’iyyar APC
- Shugaban APC na kasa, ya yaba wa Dr. Mariya, wacce ita ce karamar ministar Abuja, bisa jajircewarta wajen tallafawa addini da sauran jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara garin Bunkure, karamar hukumar Bunkure da ke jihar Kano.
Dr. Ganduje ya ziyarci garin ne domin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da karamar ministar Abuja, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta gina.

Asali: Twitter
Ganduje ya kaddamar da masallacin minista a Kano
Punch ta rahoto cewa an kaddamar da masallacin ne bayan kammala sallar Juma’ah, wanda ya samu halarar jiga-jigan APC, ciki har da shugaban jam'iyyar na Kano, Hon. Abdullahi Abbas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna a 2023, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Hon. Murtala Sule Garo sun halarta.
Sauran da suka hallara sun hada da Sanata Kawu Sumaila, Hon. Kabiru Alhassan Rurum da sauran fitattun ‘yan siyasa da jiga-jigan APC.
A jawabin da ya gabatar, Ganduje ya yabawa Dr. Mariya bisa jajircewarta wajen ci gaban addini da al’umma, yana mai cewa hakan alamar shugabanci ne na gari.
Ganduje ya yabawa ministar Abuja, Dr. Mariya
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa:
“Muna fatan wannan masallacin da ministar ta gina zai amfani al’ummar wannan gari na tsawon zamani.”
"Dr. Mariya ta nuna kyakkyawan shugabanci ta hanyar sanya dukiyarta a harkokin addini da zamantakewa. Ina kiran sauran jami’an gwamnati da su koyi da irin wannan sadaukarwa.”
Bayan kaddamar da masallacin, Ganduje ya roki Allah ya sanya wa masallacin albarka, ya saka wa Dr. Mariya da lada mai yawa tare da ƙarfafa ta a ayyukantan addini da al’umma.
An ruwaito cewa sabon masallacin zai iya daukar daruruwan masu ibada a lokaci daya tare da zama matattar karatu da haɗin kan al’umma.

Asali: Twitter
'Yan Najeriya sun yi martani ga minista
A shafin X, wani mai goyon bayan APC mai suna @tudunwada__mi ya rubuta cewa:
"Shugaban APC na ƙasa, Dr. Ganduje ya jagoranci buɗe sabon masallacin Juma’a da ministar Abuja, Dr. Mariya Bunkure ta gina a garin Bunkure.
“A siyasance, ku ji tsoron Ganduje. Ku dai duba ku gani, tsofaffin magoya bayan Kwankwaso ne gaba gaba a wannan taron.”
Wannan sakon ya jawo martanin daban daban daga masu bibiyar sa:
@adewale_ibk:
"Ashe muna da karamar ministan Abuja? Yau na fara jin hakan yau. Wike mugun ɗan siyasa ne!"
@abalivpo:
"Ba wani abun tsoro."
@BasharKara94736:
"Taron makakku ne kawai."
@e_dangana:
"Abinci muke bukata ba masallaci ba. Aikin banza kawai."
@GrandJoe9:
"Me masallaci zai ƙara wa tattalin arzikin kasa idan gwamnati ke gina shi da kudin jama’a?"
Dr. Mariya Bunkure ta canji Maryam Shetti
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, tsohuwar kwamishinar Kano ta canji matashiya, Maryam Shetti, a yayin tantance ministocin Shugaba Bola Tinubu.
Tun da fari, Shugaba Tinubu ya aike da sunan Maryam Shetti ga majalisa domin tantance ta a mukamin minsta, daga Kano, sai dai daga bisani aka cire ta, tare da mayeta da Bunkure.
Da majalisa ta gayyaci Dr. Mariya domin ta bayyana kan ta, tsohuwar kwamishinar ilmin ta shaida cewa ta gama digiri a ilmin likitanci daga jami'ar Bayero a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng