Bayan Kalaman Okowa, Atiku Ya Yi Magana kan Ficewa daga PDP

Bayan Kalaman Okowa, Atiku Ya Yi Magana kan Ficewa daga PDP

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya taɓo batun sauya sheƙar abokin takararsa a zaɓen 2023 zuwa APC
  • Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai ji zafin sauya sheƙar da Sanata Ifeanyi Okowa ya yi ba zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan a zaɓen 2023, ya kuma bayyana cewa har yanzu yana nan daram a cikin jam'iyyar PDP
  • Wazirin Adamawa ya nuna cewa babu ƙamshin gaskiya a jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan sauya sheƙar da abokin takararsa a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa, ya yi zuwa jam'iyyar APC.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba ya jin damuwa ko ɓacin rai game da sauya sheƙar Sanata Ifeanyi Okowa, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Atiku Abubakar, Ifeanyi Okowa
Atiku ya ce bai ji zafin ficewar Okowa zuwa APC ba Hoto: @atiku, @IAOkowa
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Paul Ibe, a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Atiku ya ce kan ficewar Okowa zuwa APC?

Atiku ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa ya ji ba daɗi kan mutumin da ya yi amfani da ƴancinsa na dimokuraɗiyya.

“Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ba ya ɗaukar kowa da gaba, ya faɗa hakan kuma yana nufin hakan."
"A matsayinsa na ɗan dimokuraɗiyya, yana mutunta ƴancin yin tarayya da yin zaɓi wanda shi ne ginshikin dimokuraɗiyya, ba tare da hakan ba, dimokuraɗiyya za ta zama ba ta da wata ma’ana."

- Paul Ibe

Me Atiku ya ce kan ficewa daga PDP

Ya ƙara jaddada cewa Atiku yana nan daram a cikin PDP yana mai cewa duk zancen da ake yi game da ficewarsa daga jam’iyyar zuwa wata jam’iyya wani zance ne kawai mara tushe.

Atiku Abubakar
Atiku ya ce yana nan daram a PDP Hoto: @atiku
Asali: Facebook
“Mun riga mun bayyana matsayarmu game da batun haɗaka. Ku tuna mun fitar da sanarwa a kan hakan. Alhaji Atiku Abubakar ba zai bar PDP ba, kuma ya bayyana hakan a fili."
“Game da waɗanda ke yaɗa jita-jitar cewa zai bar PDP, ba mu san inda suke samun hakan ba."

- Paul Ibe

Karanta wasu labaran kan Atiku Abubakar

An buƙaci PDP ta kori Atiku, Wike

A wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Olabode George, ya caccaki Atiku Abubakar da Nyesom Wike.

Olabode George ya zargi manyan ƴan siyasar biyu da cin dunduniyar jam'iyyar ta PDP, inda ya yi kiran da aka kore su.

Babban ƙusan na PDP ya caccaki yadda Atiku Abubakar ya wanke ƙafa ya kai ziyara a gidan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng