Siyasa Rigar 'Yanci: Jerin Gwamnonin PDP da Suka Koma APC Suna kan Mulki
- Ba a taɓo batun siyasa a Najeriya ba tare da yin magana kan yadda ƴan siyasa suke sauya sheƙa daga wannan jam'iyya zuwa wannan ba
- A shekarun da suka gabata, an samu gwamnonin jam'iyyar PDP da ke kan mulki da suka tsallaka zuwa APC mai rike da gwamnatin tarayya
- Na baya-bayan nan daga cikinsu shi ne Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta wanda ya koma APC tare da magabacinsa, Ifeanyi Okowa
- Gwamnonin dai suna ba da mabambantan dalilai da suka sanya su ɗaukar matakin ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai ci a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnoni a tarayyar Najeriya sun saba sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Sauya sheƙa dai a fagen siyasar Najeriya ba wani baƙon abu ba ne, domin ƴan siyasa sun saba tsallakawa daga wannan jam'iyya zuwa wannan.

Asali: Facebook
Gwamnonin PDP da suka koma jam'iyyar APC
A ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC mai mulki a hukumance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tsawon shekarun baya, gwamnonin PDP da dama sun sauya sheƙa zuwa APC yayin da suke kan mulki.
Ga jerin wasu daga cikinsu:
1. Sheriff Oborevwori (Jihar Delta)

Asali: Twitter
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya ba mutane mamaki bayan da ya bar PDP ya koma jam'iyyar APC a ranar Laraba, 23 ga watan Afirilun 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.
Sheriff Oborevwori ya koma jam'iyyar APC bayan an daɗe ana raɗe-raɗin cewa zai fice daga PDP mai mulki a jihar.
Sauya jam’iyyar da ya yi ya kasance babbar alama ta samun sauyin siyasa a jihar Delta, wacce PDP ke riƙe da ita tun 1999.
2. Dave Umahi (Jihar Ebonyi)

Asali: UGC
A watan Nuwamba 2020, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya koma APC bayan ya fice daga PDP a wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna.
Jaridar Premium Times ta ce ya bayyana cewa PDP ta nuna wariya ga yankin Kudu maso Gabas, sannan ya yabawa APC kan ayyukan ci gaba a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari.
3. Ben Ayade (Jihar Cross Rivers)

Asali: Facebook
Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC a watan Mayu 2021, cewar rahoton tashar Arise.
Gwamna Ayade ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP zuwa APC ne domin komawa waje ɗaya da gwamnatin tarayya don jawo ayyukan ci gaba zuwa jihar Cross River.
4. Rabiu Musa Kwankwaso

Asali: Facebook
Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya yi bankwana da jam'iyyar PDP a shekarar 2013, cewar rahoton jaridar Premium Times.
Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP.
5. Rotimi Amaechi (Jihar Rivers)

Asali: Twitter
Rotimi Amaechi na jihar Rivers na ɗaya daga cikin gwamnonin PDP da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, cewar rahoton Premium Times.
Amaechi ya bayyana cewa ya fice daga PDP ne saboda yadda gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Goodluck Jonathan, ba ta yi wa jiharsa adalci.
6. Murtala Nyako (Jihar Adamawa)

Asali: Twitter
Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai adawa.
Nyako ya bayyana cewa ya koma APC ne domin ceto Najeriya daga hannun masu mulkin kama-karya, cewar rahoton Premium Times.
7. Bello Matawalle (Jihar Zamfara)

Asali: Facebook
A watan Yunin 2021, Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, cewar rahoton tashar Channels tv.
Sauyinsa ya biyo bayan rikice-rikicen siyasa a Zamfara, kuma ana kallon hakan a matsayin dabarar siyasa don tabbatar da daidaito a jihar.
8. Aliyu Wamakko (Jihar Sokoto)

Asali: Facebook
Aliyu Magatakarda Wamakko na jihar Sokoto ya shiga jam'iyyar APC bayan ya fice daga PDP a shekarar 2013, cewar rahoton Daily Post.
Gwamna Wamakko yana daga cikin waɗanda suka fara sauya sheƙa zuwa APC tun da farko, wanda hakan ya taimaka wajen gina nasarar APC a zaɓen 2015.
Wamakko na daga cikin gwamnonin PDP na ƙungiyar G-7 da suka fice daga jam'iyyar zuwa APC kafin babban zaɓen shekarar 2015.
9. Abdulfatah Ahmed (Jihar Kwara)

Asali: Facebook
Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara wanda ya yi mulki daga 2011 zuwa 2019, ya koma APC a shekarar 2013 bayan ya fice daga PDP.
Abdulfatah Ahmed ya koma jam'iyyar APC ne tare da Bukola Saraki a cikin abin da aka kira gagarumin sauyin siyasa a jihar Kwara.
Ko da yake daga baya Gwamna Abdulfatah ya koma PDP, sauyin da ya yi a lokacin yana da matuƙar tasiri a siyasar jihar.
Mataimakin Atiku a zaɓen 2023 ya fice PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Sanata Ifeanyi Okowa, ya fice daga jam'iyyar.
Sanata Ifeanyi Okowa wanda ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a zaɓen na shekarar 2023, ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Tsohon gwamnan na jihar Delta ya koma APC ne tare da magajinsa Gwamna Sheriff Oborevwori da dukkanin kwamishinoni da masu ruwa da tsaki na PDP a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng