Salihu Lukman: Tsohon Shugaba a APC Ya Sake Dura kan Gwamnatin Bola Tinubu

Salihu Lukman: Tsohon Shugaba a APC Ya Sake Dura kan Gwamnatin Bola Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya nuna rashin gamsuwarsa da kamun ludayin Bola Tinubu
  • Salihu Lukman ya ƙalubalanci gwamnatin kan rashin samar da wani ingantaccen tsarin tattalin arziƙi da zai amfani ƴan Najeriya
  • Tsohon jigon na APC na Arewacin kasar nan ya ce ya cire tsammanin cewa gwamnatin Tinubu za ta taɓuka wani abin kirki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Salihu Lukman ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta da wani ingantaccen tsarin tattalin arziƙi da zai amfani ƙasar nan.

Salihu Lukman ya caccaki gwamnatin Tinubu
Salihu Lukman ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta tabuka komai ba Hoto: Salihu Lukman, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Salihu Lukman ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Inside Sources'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salihu Lukman ya caccaki Bola Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban na APC ya kuma ya bayyana rashin jin daɗinsa game da salon shugabancin Tinubu.

Ya soki dalilin da ya sa shugaban ƙasa ya cire tallafin fetur da kuma sakin Naira sakaka ba tare da wani ingantaccen shiri na bunkasa masana’antu da ƙarfafa samun kuɗin shiga ga ƴan ƙasa ba.

Salihu Lukman ya kuma ce Tinubu ya ware kansa domin bai bari ana ganinsa.

"Kamar ya ware kansa ne, har a cikin jam’iyya ma. Babu wanda ke sauƙin samun ganinsa, kuma wannan ba irin shugabancin ci gaba bane da nake zato zai yi."

- Salihu Lukman

Ya bayyana cewa salon mulkin Tinubu ya sha banban da irin yadda ya tafiyar da gwamnatinsa lokacin da ya kasance gwamnan Legas.

"A ra’ayina, ba haka ya tafiyar da jihar Legas ba. Na kai ga yanke shawarar cewa ba zan iya sa ran wani abin kirki zai fito daga wannan gwamnati ba."
"Na gama yanke shawarar cewa babu wani abin kirki da zai fito, kuma saboda haka dole ne mu fara shiri."

"Na faɗi haka tun da farko, wannan ƙasa za a iya gyarata a zamaninmu, kuma ina roƙon Allah Ya ba mu ƙarfin hali da ƙwarin gwiwa mu fuskanci shugabanninmu.”

- Salihu Lukman

Salihu Lukman
Salihu Lukman ya ce tuni ya dawo daga rakiyar Tinubu Hoto: Salihu Lukman
Asali: Twitter

Meyasa Salihu ya daina goyon bayan Tinubu?

Salihu Lukman ya ce ya jira har zuwa watan Yuli na bara kafin ya janye goyon bayansa ga Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar ya killace kansa, har da ƴan jam’iyyarsa, domin babu wanda ke samun damar ganinsa.

Ya ƙara da cewa kafin faruwar hakan yana da tabbacin cewa Tinubu zai gyara kura-kuren da Muhammadu Buhari ya yi.

'Dan siyasar ya ce rashin nasarar Tinubu yanzu ta sa Buhari yana kama da gwarzo a idon jama'a.

Salihu Lukman ya faɗi kuskuren El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya ce Nasir El-Rufai ya yi saurin sauya sheƙa bayan yaAPC

Salihu Lukman an ya bayyana cewa komawar tsohon gwamnan Kaduna zuwa jam'iyyar SDP, abu ne wanda ya yi cikin sauri.

Ya nuna cewa ficewarsa daga APC zuwa SDP na iya kawo cikas ga tattaunawar da ƴan adawa suke yi domin kafa haɗaka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng