PDP Ta Kasa Hakura da Sauya Shekar Gwamna Delta zuwa APC, Ta Dauki Mataki

PDP Ta Kasa Hakura da Sauya Shekar Gwamna Delta zuwa APC, Ta Dauki Mataki

  • Jam'iyyar PDP ta nuna rashin amincewarta kan sauya sheƙar da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ya bayyana cewa za su ɗauki matakin shari'a kan gwamnan tare da Sanata Ifeanyi Okowa
  • Ambasada Damagum ya bayyana cewa an umarci mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a ya fara shirin gurfanar da ƴan siyasar a gaban kotu
  • Hakazalika jam'iyyar PDP mai hanayya ta sanar da wanda zai ci gaba da jan ragamar shugabancin jam'iyyar a jihar Delta mai arziƙin mai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta shirya ɗaukar matakin shari'a kan gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da Sanata Ifeanyi Okowa.

PDP ta umurci mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar, Kamaldeen Ajibade, da ya fara shirya takardun shari’a don gurfanar da Gwamna Sheriff Oborevwori, Sanata Ifeanyi Okowa, gaban kotu kan sauya sheƙa zuwa APC.

Sheriff Oborevwori, Ifeanyi Okowa
PDP za ta kai gwamnan Delta kara gaban kotu Hoto: @RtHonSheriff, @IAOkowa
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai bayan zaman farko na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Delta ya watsawa PDP ƙasa a ido

A ranar 23 ga watan Afrilu, 2025, Sanata Ifeanyi Okowa, Gwamna Oborevwori, da shugabannin PDP na jihar Delta suka koma jam’iyyar APC.

Hakazalika mataimakin gwamnan Delta, Monday Onyeme, kwamishinonin jiha, shugabannin ƙananan hukumomi, da kuma gungun ƴan siyasa daga matakin ƙasa har sama, duk sun bi sahun sauya sheƙa zuwa APC.

Sun dai sauya sheƙar ne bayan wata ganawa ta bayan fage da suka gudanar a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Wannan sauya sheƙar ya haifar da fargaba daga jam’iyyun hamayya cewa hakan na iya sanyawa ƙasar nan ta koma ƙarƙashin jam'iyya ɗaya.

Wane mataki jam'iyyar PDP za ta ɗauka?

Umar Damagum ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta shirya shigar da ƙara a kotu domin dawo da kujerarta, kasancewar waɗanda suka sauya sheƙar sun samu nasarar zaɓe ne a ƙarƙashin tutar PDP.

Umar Damagum
PDP za ta je.kotu kan sauya shekar gwamnan Delta Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Shugaban ya ƙara da cewa an ba Emma Ogidi, shugaban riƙo na yankin Kudu maso Kudu, umarnin ɗaukar ragamar shugabancin PDP a jihar Delta, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Har ila yau, Emma Ogidi zai nemo sababbin shugabannin da za su ja ragamar jam’iyyar PDP a jihar Delta.

Atiku zai bar jam'iyyar PDP - Okowa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya taɓo batun ci gaba da zaman Atiku Abuɓakar a jam'iyyar adawa ta PDP.

Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba tsohon mataimakin shugaban ƙasan zai tattara kayansa ya fice daga PDP.

Sanata Okowa ya kuma yi watsi da shirin ƴan adawa na kafa haɗaka, inda ya ce ba ta da ƙarfin da za ta yi wani tasiri.

Hakazalika ya nuna goyon bayansa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya ci gaba da mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng