Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ya Yi Murabus? An Gano Gaskiya

Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ya Yi Murabus? An Gano Gaskiya

  • Mataimakin gwamnan Neja, Kwamared Yakubu Garba, ya fito ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya yi murabus daga muƙaminsa
  • Hadimarsa wajen yaɗa labarai, Ummikhultime Abdullahi ta musanta cewa mataimakin gwamnan ya sauka daga kan kujerarsa
  • Ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a cikin jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ya yi murabus
  • Jami'ai a ofishin mataimakin gwamnan jihar Neja sun buƙaci jama'a da su riƙa tabbatar da sahihancin labarai kafin su amince da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya yi murabus.

Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa bai yi murabus daga muƙaminsa ba, saɓanin jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Yakubu Garba
Yakuba Garba ya musanta yin murabus Hoto: @Yakubugarba
Asali: Twitter

Babbar jami'ar hulɗa da jama'a ta mataimakin gwamnan, Ummikhultume Abdullahi, ta tabbatar da hakan yayin wata zantawa da jaridar Vanguard ta wayar tarho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jita ta ce mataimakin gwamnan Neja ya yi murabus

Wasu rahotanni dai sun yi yawo a kafafen sada zumunta, inda suke cewa mataimakin gwamnan ya shirya rabuwa da kujerarsa.

A cewar rahotannin, Yakubu Garba zai yi murabus ne saboda yadda dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Gwamna Umaru Bago na jihar.

Ummikhultume Abdullahi ta ƙaryata jita-jitar, tana mai cewa ba gaskiya ba ne kuma babu ƙamshin gaskiya a cikinta.

Ta tabbatar da cewa Yakubu Garba yana nan daram a ofis, yana ci gaba da gudanar da aikinsa daga gidansa da ke kusa da gidan gwamnati a birnin Minna.

"Ina cikin gidansa a yanzu haka, yana sama, ni kuma ina ƙasa. Zan iya tabbatar muku da cewa Kwamared Yakubu Garba har yanzu shi ne mataimakin gwamnan jihar Neja. Babu wani abu makamancin murabus."

- Ummikhultume Abdullahi

Yakubu Garba yana nan daram a muƙaminsa

Ta nuna cewa babu wata tattaunawa ko abubuwan da ake yi da suke cewa zai yi murabus.

Wannan bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa mataimakin gwamnan ya ajiye aikinsa, wanda hakan ya haddasa damuwa a fagen siyasar jihar.

Jihar Neja
Mataimakin gwamnan Neja bai yi murabus ba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’ai daga ofishin mataimakin gwamnan sun roƙi jama’a da su yi watsi da irin waɗannan ƙagaggun labarai, tare da gargadin cewa yada irin waɗannan bayanai marasa tushe na iya haddasa fitina da tashin hankali a cikin al’umma.

Bayanin dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman jiran tsammani a jihar Neja, sakamakon jita-jitar cewa mataimakin gwamnan zai yi murabus.

Yadda yada jita-jita ta yi yawa a siyasar Najeriya

A duniyar siyasa, yawan jita-jita kan cewa wani ɗan siyasa ya yi murabus yawanci yana faruwa ne saboda sabani a cikin gwamnati, rashin jituwa tsakanin manyan jami'ai, ko kuma wata manufa ta ɓata suna daga abokan adawa.

Wasu lokuta, jita-jitar na fitowa daga majiyoyi marasa tushe ko kuma sakamakon fassarar kuskure na wasu abubuwa da suka faru.

Kafafen sada zumunta suna ƙara ƙarfafa yaduwar irin waɗannan jita-jita cikin gaggawa kafin a fitar da bayani na gaskiya daga hukumomi.

Misali, a shekarar 2021, an yaɗa jita-jita cewa mataimakin shugaban ƙasa na wancan lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi murabus daga kujerarsa saboda rashin jituwa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Wannan jita-jita ta bazu a kafafen sada zumunta, ta haifar da rudani a fadin ƙasa. Sai dai fadar shugaban ƙasa ta gaggauta karyata wannan labari, tana mai cewa ƙarya ce da nufin haddasa rikici.

Farfesa Osinbajo ya ci gaba da gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali, kuma wannan lamari ya nuna yadda labaran ƙarya ke yaduwa da kuma yadda za su iya shafan zaman lafiyar kasa idan ba a yi gaggawar karyata su ba.

Gwamnatin Neja ta sa dokar taƙaita zirga-zirga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja, ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a cikin birnin Minna babban birnin jihar.

Gwamnatin ta sanya dokar hana zirga-zirgar babura da keke Napep daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe.

Matakin sanya dokar taƙaita zirga-zirgar na da nufin daƙile matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng