'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Dasa Bama Bamai a Borno, an Rasa Rayukan Sojoji

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Dasa Bama Bamai a Borno, an Rasa Rayukan Sojoji

  • An shiga jimami a jihar Borno bayan ƴan ta'addan Boko Haram sun sake aikata ta'addanci na dasa bama-bamai a kan hanya
  • Miyagun yan ta'addan sun jawo asarar rayukan sojoji guda biyu bayan sun dasa bama-bamai a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri
  • Ƴan ta'addan Boko Haram na yawan dasa bama-bamai a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri wacce ba a bin ta sai da rakiyar sojoji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun dasa bama-bamai waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu a jihar Borno.

Ƴan ta'addan Boko Haram sun dasa bama-baman ne a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun dasa bama-bamai a Borno
'Yan Boko haram sun kashe sojoji a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a ranar Talata, a kusa da ƙauyen Nyeliri, wanda aka bar shi babu kowa da ke ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bam ya tashi da sojoji a jihar Borno

Fashewar ta jefa fargaba a zukatan direbobi da fasinjoji, inda suka watse zuwa sassa daban-daban duk da kasancewar suna ƙarƙashin rakiya ta dakarun sojoji.

Harin na zuwa ne ƙasa da kwana 16 bayan wasu bama-bamai da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa sun hallaka fasinjoji takwas tare da jikkata wasu da dama a hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Hanyar Maiduguri zuwa Damboa ta kasance ana amfani da ita na wucin gadi tare da rakiya ta sojoji a kullum, amma har yanzu tana cikin haɗari saboda yawan hare-haren da ƴan ta’adda ke kai wa.

A makon da ya gabata, a ranar Juma’a, 25 ga Afrilu, wasu masu sayar da gawayi guda shida sun rasa rayukansu a yankin Mulgoi.

Haka kuma, a ranar Lahadi, 27 ga watan Afrilu, wasu manoma biyu sun hallaka a hannun Boko Haram a hanyar Kanama da ke ƙaramar hukumar Damboa yayin da suke gyara gonakinsu domin shirin noman damina.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojoji biyi a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An tabbatar da aukuwar harin

Da yake tabbatar da faruwar lamarin na ranar Talata, Hakimin Damboa, Alhaji Lawan Maina, ya ce:

"Sojoji biyu sun mutu."

Ya bayyana sabbin hare-haren Boko Haram a matsayin abin tsoro wanda aka kasa ɗaukar matakin da ya dace a kansu.

Shi ma da yake mayar da martani, Sanata Mohammed Ali Ndume (APC, Kudu Borno) ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa dakarun soji da makamai na zamani domin kawo karshen kashe-kashe da lalata rayuka da dukiyoyi a yankin.

Bam ya kashe mutane a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya yi sanadiyyar rasuwar matafiya a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa bam ɗin ya jawo asarar rayukan matafiya da dama bayan ya tarwatse a kan hanyar Kala-Balge zuwa Gamboru-Ngala.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno wanda ya tabbatar da aukuwar harin, ya bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng