Halin da Ahmed Isa na Brekete Family ke ciki bayan Rade Radin Kama Shi

Halin da Ahmed Isa na Brekete Family ke ciki bayan Rade Radin Kama Shi

  • An samu bayanai kan rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kama Ahmad Isah da aka fi sani da "Ordinary President"
  • Abokin aikin shi ya bayyana cewa Ahmad Isah yana lafiya kuma yana hutu ne bayan fiye da shekaru 16 yana hidimar jama'a ba tare da hutu ba
  • An bukaci jama'a da su yi watsi da jita-jitar cewa an kama shi, su kuma ci gaba da yi masa addu'a yayin da yake hutu domin ya dawo da ƙarfi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata sanarwa daga abokin aikin Ahmad Isah, wanda aka fi sani da "Ordinary President," ta karyata jita-jitar da ke cewa an kama shi an tura shi gidan yari.

Sanarwar ta bayyana cewa Ordinary President yana cikin koshin lafiya yayin da yake yin hutu na musamman bayan shekaru da dama yana hidima ga marasa ƙarfi a Najeriya.

Ahmed Isa
Abokin aikin Ahmed Isah ya tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya. Hoto: Orginary Ahmad Isah
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an bukaci jama'a da su nisanci yada jita jita kan halin da Ahmed Isa ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abokin aikin na shi ya ce bayan kusan shekaru 16 yana hidimar jama'a ba tare da hutawa ba, Ahmad Isah ya yanke shawarar yin hutu domin samun damar murmurewa da ƙara ƙarfi.

Berekete Family: Halin da Ahmed Isa ke ciki

A Facebook ne Abdullahi O Haruna Haruspice ya bayyana cewa jita-jitar kama shi ba gaskiya ba ce, domin kuwa yana hutu ne bayan shekaru da dama yana aiki dare da rana.

Ya ce:

"Tun ƙarfe 4:00 na safe yake tashi yana shirye-shiryen tallafa wa jama'a, idan ya fara shirye-shiryen safe har sai ya kai dare.

"Ko jarumi mafi ƙarfi sai ya buƙaci hutu domin dawo da ƙarfinsa."

Ya ƙara da cewa yana fatan jama'a za su fahimci cewa Ahmed Isah yana hutu ne kuma zai dawo da ƙarfin jiki domin ci gaba da fafutukar kare hakkokin marasa galihu.

Wani malami a jami'ar ABU, Abdullahi Haruna ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Ahmad Isa yana cikin koshin lafiya.

An bukaci jama'a su yi watsi da jita-jita

Sanarwar ta yi kira ga jama'a da su guji yada jita-jita marasa tushe musamman game da mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar jama'a.

An kuma bukaci masu amfani da kafafen sada zumunta da sauran kafafen yaɗa labarai su rika tantance sahihancin bayanai kafin su yada su.

A cewar sanarwar, Ahmad Isah ba ya buƙatar jita-jita a wannan lokaci, sai addu'a da goyon baya daga jama'a domin ya dawo cikin ƙoshin lafiya da kuzari.

Ahmed Isa
Ahmed Isa zai dawo ya cigaba da gwagwarmaya. Hoto: Brekete Family
Asali: Twitter

Ahmad Isah: Jagoran kare hakkin dan Adam

Ahmad Isah ya shahara wajen kare hakkin marasa ƙarfi ta shirin Brekete Family da ke watsa shirye-shirye a rediyo da talabijin.

Shirin Brekete Family ya zama mafaka ga talakawa da ke neman adalci a Najeriya, inda ake ɗaukar koke-kokensu a gaban jama'a domin neman mafita.

Ayyukan Ordinary President

Ahmed Isa, wanda aka fi sani da Ordinary President, fitaccen ɗan jarida ne kuma mai shirya shirin Brekete Family da ke Abuja, Najeriya.

Shirin Brekete Family wani dandali ne da ke taimaka wa talakawa wajen neman adalci da kare haƙƙoƙinsu, musamman masu ƙaramin ƙarfi.

Shirin yana gudana ta rediyo da talabijin inda mutane ke bayyana korafinsu, sannan Ahmed da tawagarsa ke kokarin samo mafita ta hanyar matsa lamba ko tattaunawa da hukumomi.

Ahmed Isa ya shahara saboda irin yadda yake fuskantar matsaloli kai tsaye ba tare da tsoro ba, yana kare 'yan Najeriya da suka rasa hanyar kai ƙorafi.

Hakanan, shirin ya zama mafita ga mutane da dama da suka samu agaji daga zalunci ko cin zarafi. Duk da yake ya fuskanci suka da kalubale, Ahmed ya cigaba da jajircewa wajen yada gaskiya da taimaka wa jama'a.

A cikin shirin Brekete, ana tattaunawa kan batutuwan shari'a, azabtarwa, cin hanci da rashawa, da kuma taimakon waɗanda suka shiga mawuyacin hali.

Wannan sadaukarwa ta sa Ahmed ya sami karɓuwa sosai a zuciyar mutane da dama a Najeriya da ma waje.

Batun kama Ahmed Isah a 2021

A wani rahoton, kun ki cewa a shekarar 2021 an taba kama jagoran shirin Brekete Family mai suna Ahmed Isa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama Ordinary President ne bayan gayyatar da 'yan sanda suka masa.

Sai dai bayan kama shi da tambayoyi da aka masa, 'yan sanda sun sake shi kuma ya bayani ga masu sauraron shi kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng