Wata Sabuwa: Okowa Ya Bayyana Lokacin da Atiku Zai Fice daga Jam'iyyar PDP

Wata Sabuwa: Okowa Ya Bayyana Lokacin da Atiku Zai Fice daga Jam'iyyar PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yi watsi da batun haɗaƙar ƴan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta na tsawon shekaru
  • Okowa wanda suka yi takara tare da Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasan na dab da barin jam'iyyar PDP
  • Tsohon gwamnan ya kuma nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinuɓu domin ya ci gaba da mulkin Najeriya har tsawon shekara takwas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, ya yi magana kan shirin Atiku Abubakar na ficewa daga jam'iyyar PDP.

Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, zai bar jam’iyyar nan ba da daɗewa ba.

Ifeanyi Okowa, Atoku Abubakar
Okowa ya ce Atiku zai bar PDP Hoto: Atiku Abubakar, Kashim Shettima
Asali: Facebook

Okowa ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise Tv a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Okowa ya yi bayani kan dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki tare da Gwamna Sheriff Oborevwori da wasu muhimman shugabannin PDP daga jihar Delta.

Sanata Okowa ya ce sun yanke shawarar sauya sheƙa ne bayan shawarwari da suka ɗauki watanni suna yi, da kuma gajiya da halin da jam’iyyar PDP ke ciki.

Me Okowa ya ce kan makomar Atiku a PDP

Okowa ya kuma tabbatar da jita-jitar da ke cewa ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP a 2023 yana nazarin sauya sheƙa.

“Na tattauna batun haɗakar ƴan adawa da Atiku kafin mu sauya sheƙa zuwa APC, kuma yanzu haka yana kan hanyarsa ta ficewa daga jam’iyyar PDP."

- Ifeanyi Okowa

Okowa ya nesanta kansa daga haɗakar ƴan adawa da Atiku ke ƙoƙarin jagoranta, yana cewa babu cikakken tsari, hangen nesa a cikinta.

"Alamu sun nuna cewa har yanzu babu wani sahihin dandali da haɗakar za ta koma, kuma ba abin da ke nuna cewa haɗakar za ta iya yin ƙarfi cikin ƙanƙanin lokaci."

- Ifeanyi Okowa

Ifeanyi Okowa
Okowa ya goyi bayan tazarcen Tinubu Hoto: Dr. Ifeanyi Okowa
Asali: UGC

Sanata Okowa ya goyi bayan Shugaba Tinubu

Maimakon haka, Okowa ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai kiran a bar shi ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sake zaɓen Tinubu a 2027 zai tabbatar da adalci a tsarin karɓa-karɓa na shugaban ƙasa tsakanin yankuna, kuma zai fi amfanar Najeriya.

Alakar Ifeanyi Okowa da Atiku Abubakar

Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa sun yi aiki tare a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2023 karkashin jam’iyyar PDP.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, dangantakarsu ta kasance mai ƙarfi mai cike da haɗin kai, inda Okowa ya kasance ɗaya daga cikin manyan magoya bayan Atiku, yana ta zagayen faɗaɗa goyon baya ga burin Atiku na zama shugaban ƙasa.

Sai dai bayan faduwar su a zaɓen 2023, abubuwa suka fara canzawa a tsakaninsu. Rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar PDP, da kuma rashin daidaiton shugabanci da tsare-tsare, sun sa Okowa ya fara nesanta kansa da Atiku da kuma jam’iyyar baki ɗaya.

A yanzu, Okowa ya bayyanawa duniya cewa ba ya goyon bayan ƙoƙarin Atiku na haɗa ‘yan adawa domin fuskantar APC, yana cewa babu cikakken tsari ko hangen nesa a wannan yunƙuri.

Har ila yau, ya goyi bayan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata a bar shi ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas.

Wannan al’amari ya nuna raguwar kusancin siyasa tsakanin Atiku da Okowa, kuma yana iya zama wata alamar rugujewar babban haɗin kan da PDP ke fata ta samu.

Okowa ya yi nadamar bin Atiku a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce nadamar zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Okowa ya bayyana cewa amincewar da ya yi don zama mataimakin Atiku ya saɓa da muradin mutanen jihar Delta da ke so mulki ya juya.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tun a lokacin yaƙin neman zaɓen da suke yi ya gane cewa ya saɓa lamba game da yin takarar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng