Haramta Acaba: Hukumar FCTA Ta Ruƙurƙushe Babura Sama da 600 a Abuja

Haramta Acaba: Hukumar FCTA Ta Ruƙurƙushe Babura Sama da 600 a Abuja

  • Hukumar DRTS ta FCTA ta lalata babura 601 da aka kama a Abuja saboda keta dokar hana zirga-zirga a wasu yankunan babban birnin
  • Sakataren sufuri, Elechi Chinedum, ya ce an kafa dokar hana hawa babura ne don kare tsaro da hana aikata laifuffuka a birnin tarayya
  • Daraktan DRTS, Abdulateef Bello, ya ce kame da lalata babura zai ci gaba don dakile fashi da aikata laifi da babura ke haddasawa a Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar DRTS ta FCTA ta lalata babura 601 da aka kama bisa laifin zirga-zirga a wuraren da aka hana a babban birnin tarayya Abuja.

Sakataren ma’aikatar sufuri ta FCTA, Elechi Chinedum, ya jagoranci jami’an gwamnati wajen gudanar da aikin a wani wuri da aka tanada.

Hukumar FCTA ta bayyana dalilin lalata babura 601 da aka kama a Abuja
Hukumar FCTA na lalata baburan da aka kama a birnin tarayya Abuja. Hoto: @Authenticvoice
Asali: Twitter

Kafa dokar hana hawa babura a Abuja

Jaridar Vanguard ta rahoto Elechi ya bayyana cewa an rukurkushe baburan ne bisa dokar da FCTA ta gabatar a ranar 1 ga Janairu, 2023, karkashin tsohon minista, Muhammad Bello.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elechi Chinedum ya ce doka ce ta hana amfani da babura a wasu yankuna na Abuja, kuma an tanadi hukunci ga masu karya dokar.

Ya ce tun farko an kafa dokar ne domin kyautata tsarin birnin Abuja, amma yanzu ta koma mai yaki da matsalar tsaro da aikata laifuffuka.

“Yanzu amfani da babura ya zama barazana ga zaman lafiya da tsaro a Abuja,” inji Elechi, yana mai jaddada muhimmancin dokar.

Dalilin hana acaba da hawa babura a Abuja

Daraktan DRTS, Abdulateef Bello, ya bayyana cewa aikin kame babura da kuma lalata su zai taimaka wajen dakile cin zarafin doka da kuma kare lafiyar jama’a.

Ya tuna cewa haramcin tuka babura a birnin Abuja ya fara tun a shekarar 2006 bisa dokar hana amfani da baburan domin sana'ar 'acaba.'

Jaridar Daily Trust ta rahoto Abdulateef Bello ya ce babura suna taimaka wa masu aikata laifi, kuma hakan ya jefa al’ummar birnin Abuja cikin barazanar tsaro.

“Za mu ci gaba da lalata dukkanin baburan da aka kama ma damar kotu ta ba mu izinin yin hakan, domin zama gargadi ga masu karya doka,” inji Abdulateef Bello.
FCTA ta sha alwashin ci gaba da kamawa tare da lalata babura domin tabbatar da tsaro a Abuja
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @OfficialFCTA
Asali: Twitter

FCTA ta lalata babura 601 da aka kama

Shugaban DRTS ya ce wadannan babura 601 da aka lalata su ne rukunin farko da aka lalata a shekarar 2025, kuma hakan na nuna tsayin daka na FCTA wajen tabbatar da doka.

“Babura 601 da aka kama cikin shekarar nan za a lalata su a yau, kuma wannan na daga cikin shirin hukumar na magance rashin tsaro,” inji Abdulateef.

Ya gargadi masu sana'ar acaba da su kauracewa Abuja, yana mai cewa gwamnati ba za ta daina daukar mataki mai tsauri ba idan ta kama baburansu.

Abdulateef Bello ya jaddada cewa DRTS za ta ci gaba da sa ido a titunan Abuja don tabbatar da cewa doka tana aiki yadda ya kamata.

FCTA ta lalata babura 1,700 a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FCTA ta lalata fiye da babura 1,700 da aka kama, yayin aiwatar da haramcin aikin 'yan acaba (Okada) a Abuja.

Daraktan hukumar kula da zirga-zirga ta FCTA, Dr. Abdulateef Bello, ya ce murkushe baburan wani mataki ne na gargadi ga masu karya doka da oda.

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta bayyana cewa an kama baburan ne sakamakon aikata miyagun laifuka da ake yi ta amfani da su a babban birnin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.