Manyan Labarai A Yau
Gwamnonin Arewacin Najeriya sun nuna amincewarsu da samar da rundunar 'yan sandan jihohi. Sun bukaci majalisar tarayya ta gaggauta daukar mataki kan hakan.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa ƴan Najeriya su ga canji a shekaru biyu da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan karagar mulki.
Gwamnonin jihohin Arewa sun gudanar da taro kan matsalolin da suka addabi yankin. Sun ba gwamnati shawara kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu da 'yan ta'adda a jihar Katsina. Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da kwato makamai da dama.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bukaci sojojin Najeriya su maida hankali kan tattara bayanan sirri. Gwamnan ya ce yin hakan zai taimaka wajen magance rashin tsaro.
Wani babban jigo a jam'iyyar PDP a jihar Edo, Chief Tom Irehovbude, ya sauya sheka zuwa APC. Tsohon jigon na PDP ya koma APC ne tare da magoya bayansa.
Dan majalisar wakilai daga jihar Neja, Hon Adamu Lokoja, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Ya samu tarba daba shugabannin APC na jihar.
Allah Ya karbi ran surukar shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen Marigayiyar ta yi bankwana da duniya ne tana da shekara 85 a daren ranar Alhamis.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan zargin da ake yi na cewa ana neman maida Najeriya kasa mai jam'iyya daya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari