Gwamna Ya Samo Mafita ga Sojoji kan Matsalar Rashin Tsaro
- Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya
- Alex Otti ya buƙaci dakarun sojojin Najeriya da su maida hankali wajen tattara bayanan sirri domin magance rashin tsaro
- Ya nuna cewa samun bayanan sirri zai taimaka matuƙa gaya wajen daƙile matsalar tun kafin ta auku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ja hankalin jami’an rundunar sojojin Najeriya kan matsalar rashin tsaro.
Gwamna Otti ya buƙaci sojojin da su maida hankali sosai wajen tattara bayanan sirri domin daƙile matsalolin rashin tsaro tun kafin su afku.

Asali: Twitter
Gwamna Otti ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a, lokacin da yake karɓar wata tawaga daga ɗaliban makarantar kwamandoji da ma’aikata ta rundunar sojojin Najeriya, cewar rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar na ƙarƙashin jagorancin kwamanda kuma daraktan nazari na makarantar, Rear Admiral Ufieko Uko, rahoton The Cable ya tabbatar.
Wace shawara Gwamna Otti ya ba sojoji?
Gwamnan ya tunatar da su cewa idan za a yi amfani da bayanan sirri yadda ya dace, to hukumomin tsaro a Najeriya za su iya daƙile laifuka da kuma magance matsalolin rashin tsaro tun kafin su faru.
"Akai-akai, idan kuka ba wa bayanan sirri muhimmanci, za ku iya hana yawancin waɗannan abubuwa kafin su faru."
"Saboda haka, ku maida hankali sosai kan tattara bayanan sirri. Hakan yana da kyau, kuma wannan kwas ɗin naku yana da alaƙa da hakan."
“Muna kuma da ra’ayi mai ƙarfi cewa tsaro yana farawa ne daga bayanan sirri. Idan aka tattara su yadda ya kamata, kuma aka tsara su da kyau, hakan na iya bayar da hasashen abin da zai faru da kuma sa hukumomi cikin shiri kafin matsalar ta taso."
- Gwamna Alex Otti
Gwamna Otti ya yabawa sojoji
Gwamnan ya bayyana cewa abin burgewa shi ne yadda ake samun ɗalibai daga ƙasashen waje da ke zuwa samun horo a Najeriya, yana mai cewa hakan alama ce ta amincewa da ƙwazon rundunar sojin ƙasar.

Asali: Facebook
Ya jaddada cewa rundunar sojojin Najeriya na da horo da ladabi, inda ya bayar da misali da yadda sojojin da ke Abia suka yi aiki tare da gwamnatinsa wajen kawar da laifi da ta’addanci a jihar.
Gwamna Otti ya taya ɗaliban murna da kuma gode wa jagororin makarantar saboda zaɓen Jihar Abia a matsayin wuri mai dacewa domin wannan ziyara ta karatu.
Ya tabbatar da cewa zai ci gaba da haɗa gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
Sojoji sun gwabza faɗa da ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi gagarumin artabu da ƴan bindiga a jihar Taraba.
Sojojin sun samu nasarar hallaka ɗan bindiga guda ɗaya yayin da suka fatattaki sauran zuwa cikin daji.
Jami'an tsaron sun kuma ƙwato babura da makamai daga hannun ƴan bindigan bayan sun kwashi lokaci suna artabu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng