Uba Sani Ya Tabo Batun 'Yan Sandan Jihohi, Ya Fadi Yadda Za a Takawa Gwamnoni Birki

Uba Sani Ya Tabo Batun 'Yan Sandan Jihohi, Ya Fadi Yadda Za a Takawa Gwamnoni Birki

  • Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna muhimmancin da ke tattare sa kafa rundunar ƴan sandan jihohi
  • Uba Sani ya nuna cewa za a iya yin dokar da za ta hana gwamnoni yin amfani da ƴan sandan ta yadda bai dace ba
  • Gwamnan ya nuna cewa yin hakan ya danganta ne daga masu tsayawa su tsara dokar kafa ƴan sandan jihohin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan samar da ƴan sandan jihohi a Najeriya.

Gwamna Uba Sani ya ce gwamnoni ba za su yi amfani da ƴan sandan jihohi ta hanyar da ba ta dace ba, idan dokar da za ta kafa rundunar ta tsara yadda za a hana tsoma bakin siyasa da kuma cin zarafi.

Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya yi magana kan 'yan sandan jihohi Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Arewa sun gana a Kaduna

An yi hirar ne bayan taron da ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) da majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa suka gudanar a Kaduna.

Shugabannin na Arewa sun buƙaci majalisar tarayya da ta hanzarta amincewa da ƙudirin kafa rundunar ƴan sandan jihohi.

Sai dai masu suka sun nuna fargabar cewa gwamnoni na iya amfani da wannan runduna don danne masu yin suka ko masu ra’ayoyin da suka yi saɓani da na gwamnati.

Masu goyon bayan kafa rundunar ƴan sandan jihohi na ganin cewa hakan zai ba jihohi damar tinkarar matsalolin tsaro ba tare da jiran taimakon gwamnatin tarayya ba.

Me Uba Sani ya ce kan ƴan sandan jihohi?

A yayin hirar, an tambayi Gwamna Uba Sani dangane da fargabar da ake nunawa kan kafa rundunar ƴan sandan jihohi, musamman dangane da ƙalubalen kuɗi da yiwuwar cin zarafi ko amfani da ita wajen siyasa.

Gwamnan na Kaduna ya ce masu tsara dokar za su iya rubuta ta yadda rundunar za ta mayar da hankali ne kawai kan yaƙi da laifuka.

"Dangane da batun fargaba, idan kana tsara doka, ya danganta ne da masu tsara ta."
"Ba za a samu wani cin zarafi ba idan an tsara dokar ta yadda ba za ta bai wa gwamnoni damar yin amfani da ita wajen cutarwa ba. Wannan shi ne mafita."
“Masu tsara dokar za su iya bayyanawa ƙarara cewa aikin rundunar zai ta’allaƙa ne kawai ga yaƙi da laifuka ba siyasa ba."
"Mu daina mayar da hankali kan siyasa mu mayar da hankali kan magance matsalar tsaro."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya nuna muhimmancin tsaro

Uba Sani
Uba Sani ya ce tsaro na da muhimmanci Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Gwamna Uba Sani ya ce ba tare da tsaro ba, ba za a iya magance matsalolin da suka shafi kiwon lafiya, ilmi da ababen more rayuwa ba.

“Matsalar tsaro na da matuƙar muhimmanci idan muna maganar kiwon lafiya, ilmi da kuma ababen more rayuwa."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya magantu kan rikici a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan rikici ƙabilanci a jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa jihar Kaduna ta yi lafiya domin ba a samu rikicin ƙabilanci ba a cikin shekara biyu da suka gabata.

Ya ce an cimma hakan ne sakamakon rawar da shugabannin gargsjiya suke takawa wajen ganin zaman lafiya ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng