Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu kan Samar da 'Yan Sandan Jihohi

Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu kan Samar da 'Yan Sandan Jihohi

  • Ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta gudanar da taro kan matsalolin da suka addabi yankin a ranar Asabar, 10 ga watan Mayun 2025 a Kaduna
  • Daga abin da gwamnonin guda 19 na jihohin Arewa suka cimmawa har da amincewa da kafa rundunar ƴan sandan jihohi
  • Gwamnonin sun kuma yabawa shugaban ƙasa bisa yadda ya jajirce wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnonin jihohi 19 na Arewa ƙarƙashin inuwar ƙungiyar gwamnonin Arewa (NGSF) sun yi magana kan kafa ƴan sandan jihohi.

Gwamnonin na Arewa sun amince da ƙirƙirar ƴan sandan jihohi bayan sun yi taro a Kaduna.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa sun goyi bayan kafa 'yan sandan jihohi Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a ƙarshen taronsu da aka gudanar ranar Asabar a Gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya fitar da sanarwar bayan taron.

Me suka ce kan ƴan sandan jihohi?

Ƙungiyar ta bayyana goyon bayanta ga samar da rundunar ƴan sandan jihohi, tana mai jaddada buƙatar tsara tsarin tsaro ta yadda za a iya fuskantar matsalolin tsaro cikin sauƙi, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

A cewar sanarwar bayan taron da aka fitar, gwamnonin sun yi kira ga majalisar tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin kafawa da aiwatar da tsarin doka da zai bada damar ƙirƙirar ƴan sandan jihohi.

"Muna sake jaddada goyon bayanmu ga kafa rundunar ƴan sandan jihohi tare da kiran majalisar tarayya da ta hanzarta kafa tsarin dokar da zai ba da dama ga fara aiwatar da hakan."

- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya

Yankin Arewa na fama da ƙalubalen tsaro iri-iri da suka haɗa da hare-haren ƴan bindiga, garkuwa da mutane da kuma ta’addanci.

Gwamnonin Arewa sun taɓo batun rashin tsaro

Gwamnonin sun amince cewa haɗin kai tare da yin haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen magance waɗannan matsalolin.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa sun gudanar da taro a Kaduna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Sanarwar ta jaddada buƙatar ɗaukar matakin haɗin kai domin tinkarar ƙalubalen tsaro da ke addabar yankin.

Gwamnonin sun kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa wajen magance matsalolin tsaro da ƙarin himma wajen samar da ababen more rayuwa a Arewa.

"Ƙungiyar ta yabawa mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa ci gaba da jajircewarsa da mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da gibin ababen more rayuwa a Arewacin Najeriya."

- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya

Gwamnonin Arewa sun magantu kan tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jihohin Arewa sun yi magana da babbar murya kan matsalar rashin tsaron da ke ci wa yankin tuwo a ƙwarya.

Gwamnonin waɗanda suka gudanar da taro a Kaduna sun buƙaci a sake duba dabarun da ake amfani da su wajen tunkalar ƙalubalen rashin tsaron da ake ta fama da shi.

Hakazalika sun nuna danuwarsu kan dawowar ayyukan ƴan ta'addan Boko a yankin Arewa maso Gabas tare da kashe-kashen da aka yi a yankin Arewa ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng