An zo wajen: Uwargidan Jonathan Ta Yi Magana kan Komawa Villa a 2027

An zo wajen: Uwargidan Jonathan Ta Yi Magana kan Komawa Villa a 2027

  • Uwargidan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ta bayyana cewa ba ta da niyyar sake komawa fadar Aso Rock Villa
  • Dame Patience Jonathan ta kuma yi magana kan tsarin karɓa-karɓa da ake amfani da shi wajen mulkin ƙasar nan
  • Ta kuma yi magana kan alaƙarsu da uwargidan mai girma shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Dame Patience Jonathan, ta bayyana cewa ba ta da niyyar komawa Aso Rock.

Patience Jonathan ta jaddada cikakken goyon bayanta ga uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, yayin da ƙasar nan ke shirin tunkarar zaɓen gama-gari na shekarar 2027.

Patience Jonathan
Patience Jonathan ta ce ba ta da niyyar komawa Villa a 2027 Hoto: @Abdullahayofel
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce ta bayyana hakan ne a daren Asabar a birnin Abuja, inda ta karɓi lambar yabo ta 'Jagorar matan shekara ta 2025' daga kamfanin Accolade Dynamics Limited.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Patience Jonathan na goyon bayan karɓa-karɓa

A wajen taron, Patience Jonathan ta sake jaddada goyon bayanta ga mulkin karɓa-karɓa, tana mai cewa tsarin karɓa-karɓa, yana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

"Ni na yarda da shugaban ƙasa guda ɗaya. Na yarda da karɓa-karɓa. Idan lokacin ka ne, zan goya maka baya. Idan ba lokacin ka ba ne, ka ja baya, domin ƙasa ta ci gaba."

- Dame Patience Jonathan

Patience Jonathan ta kuma yi magana kan kasancewar Folashade Tinubu-Ojo, ƴar Shugaba Bola Tinubu kuma Iyaloja-General ta Najeriya a wajen taron, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Ai da ita zan fara, amma na bar ta zuwa ƙarshe, ƴar shugaban ƙasanmu mai albarka, shugaban Najeriya guda ɗaya da muka yarda da shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
"Iyaloja, mun gode da tsayawa da mata, domin waɗannan matan na ki ne. Ki riƙe su sosai, suna tare da ke."

“Daga farko har ƙarshe, muna tare da ke. Babu ja da baya. Za mu bi ki. Ki nuna hanya, za mu bi. Domin shugaban ƙasa ɗaya muke da shi a lokaci guda. Ba mu da biyu."
"Ni fa ba na ɓoye magana, idan ban son wani abu, zan faɗa. Amma idan ina son wani abu, zan tsaya tsayin daka."

- Dame Patience Jonathan

Me Patience Jonathan ta ce kan Remi Tinubu

Yayin da take tunawa da tsohuwar dangantakarta da Sanata Remi Tinubu, Patience Jonathan ta bayyana cewa sun daɗe suna tare tun daga lokacin da su ke matan gwamnoni kafin kowannensu ya je Aso Rock.

Dame Patience Jonathan
Patience Jonathan ta ce ba za ta koma Villa ba Hoto: Dame Patience Jonathan
Asali: Getty Images

Ta sake jaddada cewa tana goyon bayan uwargidan shugaban ƙasa kuma ta ƙaryata duk wata jita-jita cewa tana shirin komawa siyasa ko dawowa Aso Rock Villa.

"Ina tare da ƙawata. Kawata babbar mace ce. Na ce mata zan yi kamfen da ita. Ba na ɓoyewa. Ba zan yi takara ba. Ba zan koma Villa ba. Ko kun kira ni, ba zan je ba."

- Dame Patience Jonathan

An buƙaci Jonathan ya fito takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa an buƙaci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya fito takara a zaɓen 2027.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar NRMO, Dr. Jibril Mustapha wanda yake ɗan a mutun Muhammadu Buhari.

Dr. Jirbil Mustapha ya bayyana cewa lokaci ya yi da tsohon shugaban ƙasan zai amsa kiran da ake yi masa na sake neman shugabancin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng