Manyan Labarai A Yau
Bill Gates ya zargi Elon Musk da kashe yaran talakawa a fadin duniya ta hanyar dakatar da ayyukan hukumar USAID. Gates ya ce zai rufe gidauniyarsa a 2045.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo kan ayyukan ci gaba da yake gudanarwa a jihar. Ya ce yana da hangen nesa.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake yin rashi na wasu mambobinta a majalisar wakilai. 'Yan majalisar wadanda suka fito daga Katsina sun koma APC.
Kungiyar matasan Arewa ta AYCF ta taso 'yan siyasan yankin masu sukar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a gaba. Ta ce suna jin haushi ne.
Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru, ya bayyana nasarorin da dakarun sojoji suka samu kan 'yan ta'adda. Ya ce sojoji sun hallaka dubunnan 'yan ta'adda.
Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya bayyana cewa dalilinsa na barin PDP zuwa jam'iyyar APC bai da nasaba da jam'iyya.
Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya musanta ikirarin da wasu 'yan majalisa suka yi na cewa makaman 'yan ta'adda sun fi na dakarun sojoji.
Shugaban ƙungiyar ɗalibai ta Najeriya (NANS), Atiku Abubakar Isah, ya nemi afuwar ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu da ministan matasa kan kazafin da ya masu.
Masanin tattalin arziki, Farfesa Pat Utomi, ya ƙaddamar da gwamnatin sa ido a Najeriya. Sai dai ministan yada labarai ya ce hakan kuskure ne domin ya saba wa doka.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari