Kuma dai: 'Dan Majalisar Wakilai na PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC

Kuma dai: 'Dan Majalisar Wakilai na PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Neja ya yi ƙaura daga jam'iyyar PDP mai adawa zuwa APC mai mulki
  • Hon. Adamu Lokoja ya samu tarba daga wajen shugabannin APC na jihar Neja bayan ya tattaro ƴan komatsansa daga PDP
  • Sauya sheƙar da ya yi ta sanya adadin ƴan majalisar wakilai da suka fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC ya ƙaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Neja, Hon. Adamu Lokoja, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Adamu Lokoja yana wakiltar mazaɓar Suleja, Gurara da Tafa a majalisar wakilan Najeriya.

PDP ta rasa dan majalisa daga jihar Neja
Dan majalisar.wakilai daga Neja ya koma APC Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Shugaban APC na jihar Neja, Alhaji Aminu Bobi, ne ya karɓe shi a hukumance cikin jam’iyyar APC a hedkwatar jam’iyyar da ke Minna, babban birnin jihar Neja, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta samu ƙaruwa a jihar Neja

Yayin taron tarba da aka gudanar cikin girmamawa, shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Neja ta Gabas, Danladi Ahijoh, na daga cikin waɗanda suka yi bayani.

Ya bayyana cewa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC tamkar saka jari ne ga duk wani ɗan siyasa da ke da buri da sha’awar kasancewa cikin waɗanda za a riƙa damawa da su a nan gaba.

A cewarsa, dalilan da suka jawo sauya sheƙar Hon. Adamu Lokoja sun haɗa da manufofin ci gaba da sauya fasalin mulki da ake gani a ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar APC.

Ya ce babu shakka sauya sheƙar nan wani ɓangare ne na yunƙurin da ƴan siyasa ke yi domin samun mafita daga rikice-rikicen cikin gida da rashin daidaituwar shugabanci da suka addabi jam’iyyar PDP na dogon lokaci.

Hon. Adamu Lokoja na daga cikin ƴan majalisar wakilai uku daga jihar Neja da suka samu nasarar lashe zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a majalisa ta 10, kafin daga bisani ya yanke shawarar sauya sheƙa.

PDP ta rasa dan majalisa a Neja
Daya daga cikin 'yan majalisar na PDP a Neja ya koma APC Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan majalisar PDP na komawa APC

A baya-bayan nan, ƴan majalisa guda uku daga jihar Katsina su ma sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda suka bayyana cewa rikicin cikin gida da rashin magance matsalolin da ke damun jam’iyyar ne ya sa suka bar PDP.

Wannan lamari ya ƙara nuna irin ƙalubalen da PDP ke fuskanta na riƙe mambobinta da tasirinta a siyasa, musamman a daidai lokacin da ƙasar nan ke tunkarar manyan zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Wannan ci gaba ya nuna cewa siyasar Najeriya tana da saurin canzawa bisa yanayin jam’iyyu da kyawawan manufofi da kuma jagoranci nagari.

Ganduje ya magantu kan yin jam'iyya ɗaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya taɓo batun maida Najeriya ƙasa mai jam'iyya ɗaya.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa yawan jam'iyyu a ƙasa na kawo naƙasu wajen gudanar da shugabanci.

Ya bayyana cewa idan har yin jam'iyya ɗaya shi ne abin da ƴan Najeriya suke so, to ko kaɗan ba za su yi adawa da hakan ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng