Sanata Ahmad Lawan Ya Yi Martani kan Zargin Sanyawa a Cafke Mai Sukar Ayyukansa

Sanata Ahmad Lawan Ya Yi Martani kan Zargin Sanyawa a Cafke Mai Sukar Ayyukansa

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya fito ya kare kansa kan zargin sanyawa a cafke mai sukarsa
  • Sanata Ahmad Lawan wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana cewa ko ƙaɗan babu ƙamshin gaskiya a zargin
  • Ya nuna cewa a tarihin siyarsa bai taɓa amfani da ofishinsa domin hana masu abin faɗa faɗin albarƙacin bakinsu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Sanata mai wakiltar mazaɓar Yobe ta Arewa, Sanata Ahmad Lawan, ya ƙaryata zargin da ke cewa ya bayar da umarnin kama wani ɗan mazabarsa mai suna Ishe’u Ibrahim Jadda.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama Jadda ne ta hannun jami’an tsaro bayan ya yi suka kan aikin samar da ruwa a Gashua, inda ya yi zargin cewa aikin bai samar da ruwa ba kamar yadda aka yi alƙawari.

Sanata Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan ya musanta sanyawa a cafke dan mazabarsa Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

Sanata Ahmad Lawan ya musanta sanyawa a kama mutumin ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo, ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ezrel Tabiowo ya bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattawan ba zai taɓa amfani da ofishinsa ko tasirinsa wajen danne ra’ayi ko tsoratar da masu suka ba, rahoton Daily Post ya tabbatar.

An zargi Ahmad Lawan na nuna danniya

Wannan furuci na Sanata Ahmad Lawan ya biyo bayan rahoton wata kafar yaɗa labarai da ke zargin shi da hannu wajen kama Jadda bisa maganganunsa kan aikin ruwan Gashua.

A cewar Ezrel Tabiowo, aikin ruwan da aka gudanar a garin Gashua da ke jihar Yobe, wanda Sanatan ya taimaka wajen samuwarsa, tuni gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shi tare da miƙa shi ga gwamnatin jihar don ci gaba da kula da shi.

Sai dai, mai magana da yawun Sanata Ahmad Lawan bai bayyana ko aikin yana aiki yadda ya kamata ba a halin yanzu ba.

Sanata Ahmad Lawan ya kare kansa

Sanata Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan ya musanta nuna fin karfi Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook
"Wannan wallafa mara tushe da rashin gaskiya wani ƙoƙari ne da aka tsara don ɓata sunan sanatan wanda dukkan aikinsa na hidimar jama’a ya ta’allaka ne da bin doka, tsare-tsaren dimokuradiyya, da kare haƙƙin ƴan ƙasa na faɗin albarkacin baki."
“Don kawar da duk wani ruɗani, Sanata Ahmad Lawan, ƙwararren ɗan majalisa kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, ba ya kuma ba zai taɓa amfani da ofishinsa ko tasirinsa don danne ra’ayi ko tsoratar da masu suka ba."
"Tarihinsa a matsayin ɗan majalisa har ma a lokacin da yake cikin ƴan adawa ya nuna mutum ne da ke mutunta ra’ayoyi masu bambanci da kuma kare martabar tattaunawa ta dimokuradiyya."
"Ya kamata a tuna cewa lokacin da ya shugabanci majalisar dattawa ta tara daga shekarar 2019 zuwa 2023, Sanata Ahmad Lawan ya jagoranci zauren inda ake tattaunawa cikin ƴanci tare da goyon bayan ra’ayoyi masu saɓani."

“Don haka yin zargin cewa mutum irin wannan zai shirya kama wani ɗan mazaɓarsa bisa amfani da haƙƙinsa na faɗin albarkacin baki abu ne marar tushe kuma cin mutuncin shekarun da ya yi yana hidima ta gaskiya."
“Maimakon jin tsoron suka, Sanata Ahmad Lawan na maraba da sahihin ra’ayi da ba da shawara a matsayin muhimmin abu wajen kyautata aikace-aikacen gwamnati.
“Don haka, zargin cewa yana da hannu a wani nau’i na danniya ƙarya ne kawai, kuma ƙoƙari ne da aka tsara domin karƙatar da hankali daga ci gaban da ake samu a Yobe ta Arewa."

- Ezrel Tabiowo

Ahmad Lawan ya magantu kan ficewa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi martani kan raɗe-raɗin da ke cewa yana shirin barin jam'iyyar APC

Sanata Ahmad Lawan ya bayyana ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin jitar-jitar wacce aka riƙa yaɗawa.

Ya nuna cewa zai ci gaba da zama a APC domin bai da shirin komawa jam'iyyar adawa ta SDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng