A Karshe, Amurka Ta Tausayawa Najeriya bayan Shekaru 12 da Kakaba Dokar CoE

A Karshe, Amurka Ta Tausayawa Najeriya bayan Shekaru 12 da Kakaba Dokar CoE

  • Jami’an tsaron gabar tekun Amurka sun ɗage sharuɗɗan tsaro na musamman da aka kakaba wa jiragen ruwa da ke zuwa daga Najeriya
  • Matakin ya kawo ƙarshen tsarin ƙarin tsaro da aka shafe shekaru 12 ana amfani da shi kan jiragen da ke zuwa tashoshin jiragen ruwa na Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya ta ce matakin zai ƙara wa tashoshin jiragen ruwa damar yin gogayya tare da rage kuɗaɗen jigilar kaya da jinkiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jami’an Tsaron Gabar Tekun Amurka (USCG) sun ɗage dokar CoE da aka kakaba wa jiragen ruwa da ke zuwa Amurka daga Najeriya.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen tsarin ƙarin buƙatun tsaro da aka shafe shekaru 12 ana amfani da shi kan jiragen da ke ziyartar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.

Kara karanta wannan

An turo tallafin sama da Fan miliyan 2 daga nahiyar Turai zuwa Najeriya da wasu ƙasashe 3

Oyetola.
Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Teku, Dr Adegboyega Oyetola Hoto: @Oyetola
Source: Twitter

Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Teku, Dr Adegboyega Oyetola, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja, kamsr yadda Leadership ta ruwaito.

Ya ce matakin babban ci gaba ne ga ɓangaren harkokin ruwa na Najeriya da kuma tabbatar da ci gaban da ƙasar ta samu wajen ƙarfafa tsaron ruwa da aiwatar da tsarin tsaron ruwa na ISPS.

Amurka ta cire wa Najeriya takunkumi

Dokar CoE, wanda ta fara aiki a ranar 25 ga Yunin 2014, ta tilasta wa jiragen ruwa da ke zuwa Amurka waɗanda suka taɓa ziyartar wasu tashoshin jiragen ruwa na Najeriya bin ƙarin matakan tsaro na bincike mai tsauri kafin a ba su damar shiga ruwan Amurka.

A cewar Oyetola, ɗage takunkumin ya biyo bayan ƙoƙarin da Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Teku ta Tarayya ta shafe lokaci tana yi ta hannun Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NIMASA).

Kara karanta wannan

Yadda Najeriya ta fara shirin kera makamai da motoci masu sulke

“Ɗage takunkumin fokar CoE babban mataki ne ga ɓangaren harkokin ruwa na Najeriya. Yana nuna ci gaban da muka samu wajen ƙarfafa tsaron ruwa da aiwatar da ISPS a tashoshinmu,” in ji Oyetola.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta himmatu wajen ci gaba da wannan nasara domin tabbatar da cewa Najeriya ta kasance ƙasa mai aminci, tsaro da kuma gasa wajen harkokin jigilar kaya na ƙasa da ƙasa.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin hira da manema labarai a fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

An shafe shekaru 12 da takunkumin

Fiye da shekaru goma, jiragen ruwa da ke jigilar kaya tsakanin Najeriya da Amurka suna fuskantar ƙarin buƙatun tsaro da na gudanar da ayyuka saboda tssrin CoE.

Matakan sun ƙara wa masu jigilar kaya kuɗaɗe saboda ƙarin sharuddan tsaro, bincike da takardu, tare da haifar da jinkirin sauke da ɗora kaya da kuma ƙarin damuwa kan kuɗaɗen jigilar kaya da inshora.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaron harkokin ruwa na Najeriya da kuma tabbatar da bin ka'idojin kasa da kasa, kamar yadda Punch ta rahoto.

Najeriya ta musanta rahoton Amurka

A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi fatali da rahoton Amurka, wanda ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin kudin Najeriya.

Ta ce sabon rahoton Amurka kan bayyana harkokin kudin Najeriya bai yi cikakken nazari da tantance sauye-sauyen da gwamnatin kasar ke aiwatarwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262