An Kara Yi Wa PDP Illa bayan Babban Jigo a Jam'iyya Ya Koma APC
- Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta yi rashi na ɗaya daga cikin manyan ƙusoshinta wanda ya fice zuwa APC mai mulki
- Chief Tom Irehovbude ya tattara ƴan komatsansa zuwa APC tare da ɗumbin magoya bayansa
- Tsohon jigon na jam'iyyar PDP ya nuna cewa ayyukan ci gaba da Gwamna Monday Okpepholo ke yi ne suka jawo shi zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Edo ta rasa ɗaya daga cikin fitattun jigoginta, Chief Tom Irehovbude.
Chief Tom Irehovbude ya tattara kayansa ya koma APC bayan ya fice daga jam'iyyar PDP.

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta ce ya jagoranci dubban magoya bayan PDP wajen komawa cikin jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙusa a PDP ya koma jam'iyyar APC a Edo
Chief Irehovbude, wanda ake kira Egbonghon na Ekpoma, sananne ne wajen haɗa kan jama'a daga ƙaramar hukumar Esan ta Yamma.
Yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar APC da magoya baya, Chief Irehovbude ya bayyana cewa salon jagoranci da nasarorin ci gaba da Gwamna Monday Okpebholo ke samu ne suka jawo hankalinsa har ya yanke shawarar shiga APC.
"Na shiga jam’iyyar APC ne saboda abubuwan alheri da nake ganin Gwamna Monday Okpebholo na yi, yana taɓa rayuwar mutane, yana kawo ci gaba mai ma’ana kuma yana kusantar da gwamnati ga al’umma."
"Ina goyon bayan irin wannan shugabanci nagari, kuma a shirye nake na bayar da gudummawa domin cimma wannan buri.”
- Chief Tom Irehovbude
Yayin da yake yabawa salon shugabancin Gwamna Okpebholo, Chief Irehovbude ya bayyana mulkin jam’iyyar APC a matsayin sabuwar iska mai daɗi, tare da bayar da cikakken goyon bayansa ga gwamnan da kuma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya yi alƙawarin kawo nasara a mazabarsa ga jam’iyyar APC a zaɓen da ke tafe.
"Wannan tafiya ce domin jin daɗin jama’armu. Zan yi aiki tare da APC domin tabbatar da an samu cigaba da walwala ko’ina a ƙasarmu. Kuma a shekarar 2027, za mu tsaya tsayin daka tare da Shugaba Tinubu domin ɗorewar shugabanci mai ma’ana.”
- Chief Tom Irehovbude

Asali: Original
An yaba da sauyar sheƙar jigon PDP zuwa APC
Wannan sauya sheƙa, wanda da dama ke kallonsa a matsayin nasarar siyasa ga jam’iyyar APC, ya nuna sauyin yanayin siyasar jihar Edo, musamman a yankin Edo ta Tsakiya.
Jagororin jam’iyyar sun yaba da wannan ci gaba, suna masu cewa hakan ya ƙara nuna karɓuwa da farin jinin Gwamna Okpebholo, tare da alamun cewa sauran fitattun ƴan siyasa ma za su biyo baya.
Magoya baya sun fantsama cikin murna da shagulgula bayan sanarwar, inda suka bayyana sauya shekar Chief Irehovbude a matsayin wani abu da aka dade ana jira.
Ɗan majalisar PDP ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Neja na jam'iyyar PDP, Adamu Lokoja, ya koma APC.
Adamu Lokoja ya samu tarba daga wajen shugabannin APC na jihar Neja bayan ya koma jam'iyyar mai mulki.
Ɗan majalisar dai yana ɗaya daga cikin ƴan jam'iyyar adawa da suka lashe zaɓe a jihar Neja a shekarar 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng