Dakarun Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'adda a Katsina, an Samu Asarar Rayuka

Dakarun Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'adda a Katsina, an Samu Asarar Rayuka

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kutsa cikin daji inda suka yi artabu mai zafi da ƴan ta'adda masu ɗauke da makamai a jihar Katsina
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda masu yawa tare da ƙwato makamai da kayan aikin da suke amfani da su
  • Dakarun sojojin sun kuma lalata sansanin ƴan ta'addan bayan sun fatattaki sauran zuwa cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Forest Yaki (OPFY) sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda da dama a jihar Katsina.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato bindigogi da harsasai masu yawa a wani samame da suka kai a wasu sassan jihar Katsina.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Katsina
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Katsina Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda a Katsina

Aikin tsaftace yankin daga ƴan ta’adda ya gudana ne da safiyar ranar Juma'a, 9 ga watan Mayu, da misalin ƙarfe 5:30 na safe.

Wata majiya daga sashen sojoji ta bayyana cewa dakarun sun fara farmakin ne daga ƙauyen Bini da ke cikin yankin HAR.

An ji cewaa sannan suka wuce ta Landal, Akuzo, har suka isa yankin Yan Wutsiya, inda suka ci karo da ƴan ta’addan a wani sansani da ake kira “Soja Camp.”

A lokacin samamen, dakarun sojoji sun buɗe wuta kan ƴan ta'addan, wanda ya hakan ya haifar da artabu mai tsanani.

Sojojin sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin ƴan ta’addan, yayin da sauran suka tsere cikin daji, wasu daga cikinsu ɗauƙe da raunukan harbin bindiga.

Hakan ya tabbata daga ganin jinin da ya zubo a wurare daban-daban a sansanin.

Bayan kammala artabun, sojojin sun ci gaba da bincike a sansanin kuma suka gano muhimman abubuwa da ƴan ta'addan ke amfani da su.

Dakarun Sojoji sun ƙwato makamai

Abubuwan da suka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, gidan harsashi na bindigar AK-47 guda 10 cike da harsasai 300 masu kaurin 7.62mm.

Sauran sun haɗa da bindigar PKT da aka kera cikin gida, bindiga karama da aka kera cikin gida, kayan sojoji da na'urar sadarwa ta Baofeng da cajar ta.

Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda a Katsina
Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Baya ga haka, sojojin sun lalata babur ɗin daya daga cikin ƴan ta’addan da suka tsere, tare da rushe duk wasu gine-gine da ke taimakawa rayuwar ƴan ta’addan a sansanin.

Sojojin sun jaddada aniyarsu na ci gaba da kai hare-hare har sai an tarwatsa dukkan sansanonin ‘yan ta’adda a yankin.

Wannan aiki wani babban ci gaba ne a yunkurin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Katsina da kewaye.

Gwamna Otti ya ba sojoji shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya koma mai ba dakarun sojojin Najeriya shawara.

Gwamna Otti ya shawarci sojojin Najeriya da su maida hankali wajen tattara bayanan sirri don hana aukuwar hare-haren ta'addanci.

Alex Otti ya yi nuni da cewa idan jami'an tsaron suna tattara bayanan sirri, za su iya daƙile matsalolin rashin tsaro tun kafin su afku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng