Duniyar Kwallo Za Ta Yi Kewa, Ronaldo Ya Yi Maganar Lokacin Daina Buga Wasa
- Shahararren dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya nuna alamun zai yi ritaya daga buga tamola
- Cristiano Ronaldo ya auri budurwarsa ta dogon lokaci, Georgina Rodriguez, a wani kebabben biki a kasarsa ta Portugal
- Dan wasan ya ce yana shirin jin dadin rayuwa, tafiye-tafiye da wasan padel bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Saudiyya - Cristiano Ronaldo, fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, ya yi magana kan lokacin da zai yi bankwana da buga kwallo.
Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa sabuwar kakar wasa ta bana na iya zama shekararsa ta karshe yana taka kwallon kafa.

Source: Facebook
Tashar BBC ta ce Ronaldo mai shekaru 41 ya kuma yi ishara da shirinsa na yin ritaya a wata hira da ya yi da mujallar Vogue.
Dan wasan ya auri budurwarsa ta dogon lokaci, Georgina Rodriguez, a wani karamin bikin aure da aka gudanar a Cascais, Portugal, a karshen makon da ya gabata.
An gudanar da bikin ne a ranar cika shekaru 10 da haduwar ma'auratan a karon farko. An boye bikin daga jama'a, inda rahotanni suka ce an gudanar da shi a cikin falon gidansu.
Bayan bikin, Ronaldo ya ce yana son barin gagarumin tarihi idan har ya yi ritaya daga kwallon kafa bayan kammala sabuwar kakar.
Ronaldo ya shirya barin kwallon kafa
Ronaldo ya ce:
“Wata kila wannan ita ce shekarata ta karshe a kwallon kafa, kuma ina son na bar tarihi mai girma.”
Ya kara da cewa ya riga ya tsara yadda rayuwarsa za ta kasance bayan kwallon kafa.
“Na riga na tsara makomata gaba daya. Ina da abubuwa da dama da za su shagaltar da ni, har bayyana abu guda kawai yana da wahala. Domin kwallon kafa na iya barin babban gibi, dole ne ka cike lokacinka da abubuwa daban-daban, ba abu guda kawai ba.”

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya faɗa kan matar aure da 'ya'yanta 2 cikin dare, Allah ya musu rasuwa a Kaduna
Fitaccen dan wasan da ya kafa tarihin zama wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin kwallon kafa ya ce yana son karkata hankalinsa zuwa wasu abubuwa bayan shafe shekaru 25 yana sadaukar da rayuwarsa ga wannan wasa.
Zai mai da hankali kan Padel
Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar, ya bayyana cewa zai rika buga padel, wani wasan raket da ya hada wasu abubuwa na squash, tennis da racquetball.
Wasan padel dai an kirkiro shi ne a shekarar 1969, amma ya kara samun karbuwa a shekarun baya-bayan nan.
“Zan kuma kara samun lokacin jin dadi, yin tafiye-tafiye, kallon wasan padel da kuma buga shi, wanda nake matukar so, sannan na ci gaba da jin dadin abin da na samu, abin da muka samu. Domin a karshe, shekaru 25 kenan cike da sadaukarwa.” In ji shi.

Source: Facebook
Tarihin Ronaldo a kwallon kafa
Cristiano Ronaldo ya lashe kofunan lig a Ingila, Spain, Italiya da Saudiyya, sannan ya lashe kofin UEFA Champions League sau biyar, inda shi ne kan gaba wajen yawan zura kwallaye a gasar.
Ya kuma taimaka wa tawagar Portugal ta lashe gasar UEFA European Championship da UEFA Nations League.
A halin yanzu, Ronaldo yana da kwallaye 976 a dukkanin wasannin da ya buga a rayuwarsa, kuma yana bukatar karin kwallaye 24 kacal domin ya zama dan wasan farko a hukumance da ya kai kwallaye 1,000.
Yarjejeniyar auren Ronaldo da Georgina
A wani labarin kuma, kun ji cewa Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa ta dogon lokaci, Georgina Rodríguez, sun amince da raba kadarorin da kowannensu ya mallaka kafin aure.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa kowannensu zai ci gaba da mallakar kadarorinsa daban, ma’ana gidaje da sauran abubuwan da kowannensu ya mallaka kafin aure za su ci gaba da kasancewa mallakinsa na kansa.
Asali: Legit.ng

