Wanene Gwani?: Abin da Masana Suka Ce Game da Wakokin Mamman Shata da Dauda Rarara

Wanene Gwani?: Abin da Masana Suka Ce Game da Wakokin Mamman Shata da Dauda Rarara

Katsina - Ana ci gaba da tafka muhawara a Arewacin Najeriya game da mawakin da ya fi cancanta a kira shi da "sha kundum" tsakanin marigayi Mamman Shata da Dauda Kahutu Rarara.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An fara takaddamar ne bayan da mawaki Rarara ya saki wasu wakokin siyasa da na biki a kwanakin baya, inda wasu ke ganin shi ne "shatan wannan zamani," har wasu na cewa "Rarara ya fi Shata iya waka."

Ana ci gaba da muhawa game da wakokin marigayi Mamman Shata da Dauda Kahutu Rarara
Marigayi Mamman Shata | Dauda Kahutu Rarara. Hoto: Ibrahim Sheme
Asali: Facebook

Takaddama kan wakokin Shata da Rarara

Masana adabin Hausa, musamman na fagen wakoki, ba su dauki wannan magana da wasa ba, domin kowa ya dauki alkalaminsa, ya bambance aya da tsakuwa, tsakanin Shata da Rarara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Sheme, marubuci, dan jarida, mawallafi, wanda ya yi aikin editanci a jaridu daban daban, ya bude fagen muhawarar da cewa:

"Rarara ne Shatan wannan zamanin."

A wallafar da ya yi a shafinsa na Facebook, marubucin ya kara da cewa:

"A yau, babu mawaƙin Hausa da ke tashe kamar Rarara. Zamanin shi ne, ko kana son shi ko ba ka son shi. Shi talakawa ke saurare. Shi ne zai yi yabo a ji daɗi, ya yi zambo a ji zafi.
"Yanzu ba zamanin Shata ba ne! Wani yaron ma ko Bakandamiya bai sani ba. Wanda bai fahimci haka ba, to bai san Allah ke da zamani ba!"

Wannan maganar ta sa, ta jawo martani daga mutane da dama, ciki har da Farfesa Malumfashi Ibrahim, farfesan tarihin adabin Hausa a jami'ar jihar Kaduna.

"Hada Rarara da Shata sabo ne" - Farfesa Malumfashi

Farfesa Malumfashi Ibrahim ya wallafa wani martani mai taken "Rarara da zamani," a shafinsa na Facebook cewa:

"Ƙoƙarin da wasu ke yi na kwatanta Rarara da Shata ko wasu mawaƙa na da ko na yanzu, ina ga ba bisa dandamalin nazari ba ne ake yin haka, sai dai ra'ayi da aƙida.

"A tawa fahimta kwatanta Shata da Rarara a fagen waƙa, wadda ba ta siyasa ba, babban saɓo ne, wanda ka iya kai mutane wuta, domin addinin Shata ba shi Rarara ke bi ba."

Sai dai kuma, wannan ba wai martani ne kai tsaye don kalubalantar kalaman Ibrahim Sheme ba, hasalima, shi ma Farfesa Malumfashi, ya yar da da cewa, Rarara, yana sharafinsa ne a wannan zamani.

"Duk da haka alamu ne da ke nuni da cewa an sallama wa Rarara a wannan matsayi da ya hau a wannan zamani, kwatanta shi da Shata ko Ɗanƙwairo ko wani shahararre, ai girmamawa ce, ɗaukaka ce, tabbatarwa ce ga zancen masu hikima da suke cewa zamani riga!"

- Farfesa Malumfashi Ibrahim.

Kafin mu nutsa cikin ra'ayoyin mabanbantan mutane game da 'wa ya fi wani' tsakanin Rarara da Mamman Shata, akwai bukatar nazari kan yadda kowannensu yake yin waka.

Wanene marigayi Mamman Shata?

An haifi Alhaji (Dr) Mamman Shata, fitaccen mawakin Najeriya, a shekara ta 1923 a Musawa, Jihar Katsina kuma ya rasu a ranar 18 ga watan Yuni, 1999.

Bayani daga shafin WikiPedia ya nuna cewa Mamman Shata ya sami lakabin 'Shata' daga wani mutum da ake kira Baba Salamu.

Shata a lokacin da yake saurayi yana sayar da goro, kuma bayan ya gama sayarwa sai ya raba ribar ga mutanen da ya hadu da su a kan hanyarsa ta komawa gida ko a kasuwa.

Duk lokacin da aka tambaye shi abin da ya yi da kudin da ya samu, sai ya amsa da, "Na yi shata da su," wato ya bayar da su kyauta. Sakamakon haka, Baba Salamu ya fara kiransa da 'Mai-Shata', ma'ana wanda yake kyautar da abin da ribar da ya samu.

A zantawarsa da Legit Hausa, Abubakar Sarki Muhammad, malami a sashen nazarin Hausa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jihar Kaduna, ya yi tsokaci kan 'Wanene Shata?'

Malam Abubakar Sarki ya ce:

"A gaskiya Allah ya yi wa Shata baiwa mai tarin yawa, ba kowane mawaki ya samu irin wannan baiwar ba. Shata mutum ne da yake iya kirkirar waka a nan take, ya gabatar da ita domin jama'a su ji, kuma zai yi wuya ka saurari wakokin ba ka ji dadinsu ba.

"Ya kamata a kalli Shata a matsayin 'Dan Baiwa.' Kuma wani abin burgewa da Shata shi ne, kudinka, mulkinka, sarautarka, asalinka, ba shi ba shi tsoro, kuma ba su za su sa ya yi maka waka ba."

Malam Abubakar Sarki ya yi nuni da cewa shi Mamman Shata ba mawakin gwamnati ba ne, yana yin waka ne akan abin da jama'a suke so, ba abin da gwamnati take so ba.

Malamin ya ce ko a manyan jami'o'in duniya, musamman Najeriya, an yi nazari kan wakokin Shata kuma an samu digirin koli da su, don haka ya zama mawakin Duniya ba na Najeriya kadai ba.

An ji kadan daga cikin ayyukan wakokin Dauda Kahutu Rarara
Dauda Adamu Kahutu Rarara. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

Wanene Dauda Kahutu Rarara?

An haifi Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, a jihar Katsina, a ranar 13 ga Satumba, 1986, kuma ya kasance shahararren mawakin siyasa.

Wani bayani daga shafin WikiPedia ya nuna cewa Rarara ya yi suna ne yayin babban zaben Najeriya na 2015, lokacin da yake rera wakoki ga Muhammadu Buhari da kuma adawa da shugabancin Goodluck Jonathan.

A watan satumbar 2020, Rarara ya nemi gudummuwa daga masoyan Buhari, don tura masa Naira dubu daya domin sakin bidiyon minti biyu na yabon Buhari, inda cikin kasa da awanni 48 ya karbi Naira miliyan 57.

Game da mawaki Dauda Kahutu Rarara, Malam Abubakar Sarki Muhammad ya ce:

"Na yarda Daudada Kahutu Rarara yana da fasaha, yana da murya wajen rera wakokinsa. Amma abin da nake so mutane su gane shi ne, wakokin Rarara, rubutattu ne.
"Shi ya sa a jami'a muke kiransu da wakokin zamani. Suna tare da zamani ne kawai saboda an sanya masu kida, an sanya masu amshi, kuma har anzo ana rawa. Wadannan sun zama rubutattun wakoki na zamani.
"Sannan bincike ya gwada cewa, Rarara ba ya rubuta wadannan wakoki da kansa, yana da mutanen da suke rubuta masa. Ka ga kenan, in ana maganar fasaha, to yana da fasahar rera waka ne kawai ba fasahar kirkira ba."

Me ya bambanta Mamman Shata da Rarara?

Game da bambanci tsakanin marigayi Mamman Shata da Dauda Rarara, wani marubuci a Facebook, Abubakar Shehu Dokoki, ya wallafa cewa:

"Rarara ya iya waƙa tabbas, amma yana waƙa mai "ƙafiya" ne, wadda ita ake cewa rubutacciyar waƙa, ba zaka taɓa waƙa mai ƙafiya data haura minti 10 ba ka rubuta ba, domin gudun karka ɓata.
"Mamman shata yana waƙar baka ne, waƙar da a lokacin yake yinta nan take, idan ya yi baiti ɗaya, kafin a gama amshi nan take zai yi tunanin ɗaya baitin.
"Shata yana da baiwar waƙe duk abinda ya kalla, kuma a lokacin da yake so, kama daga tsuntsu, kifi, saniya, doki, sarauta, siyasa, da sauransu. Rarara ya fi maida hankali ne a kan waƙar siyasa da kuma biki, Shata ya haɗa kowanne ɓangare.
"Shata yana taimakawa harshen Hausa, ta hanyar kawo zaurance cikin waƙa, habaici mai buƙatar fassara, da kuma magana mai harshen damo, tare da kawo kalmomin Hausa masu sarƙaƙiya."

Marubuci Ibrahim Sheme kuwa, cewa ya yi:

"To, ta yaya ma mutum zai kwatanta Shata da Rarara ta fannin basira, siga, yawan waƙoƙi, dukiya, arzikin jama'a, da tasiri mai ɗorewa a adabi - har ya ce Rarara ya kama ƙafar Shata?
"Kamar ka kwatanta Shakespeare da wani wanda ya lashe kyautar rubutun littafi ne. Idan lambar basira ko ma'ana ko tasiri a adabi a wannan zamanin zan bayar, to Aminu Ala zan ba lambar farko.
"Amma idan an ce wanne mawaƙin Hausa ne yake tashe yanzu tsakanin Shata da Rarara ko wani mawaƙin? Amsar ita ce: Dauda Rarara."

Shi kuwa fitaccen dan jaridar nan, Jaafar Jaafar, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"Bayan fasahar waƙa da Allah ya ba shi, Shata zai kawo ma tarihi ko ya ilmantar da kai wurare ko dabi’un wasu mutane a cikin waƙa. A waƙar yawon duniya, Shata ya ba da labarin abubuwan mamaki da ya gani.

"Haka zalika a waƙar zuwa Amurka, a bakin Shata muka fara jin labarin ATM wanda har ya rasu bai zo Najeriya ba. Bugu da ƙari a cikin waƙa Shata ya ba mu labarin Kumbo Apollo 11 kamar muna kallonsa da idonmu.
"Idan kana so ka san taswirar ƙasar Hausa, in ka saurari waƙar Shata ta Sarkin Daura za ka ji yadda ya zana taswirar ƙasar Hausa a cikin waƙar.
"Duk wannan fa ba wani ne ke rubuta masa ba, ba zama yake ya yi tilawa ba, ba “mimin” yake ba, ba zaɓar murya mai zaƙi yake a sitadiyo ba!
"Idan za ka auna Rarara bisa doron ilimi sai dai ka sa shi a layin makaɗan siyasa irin su Auwalu Bunguɗu ko Musa Ɗanba’u ko kuma a layin makadan ɓarayi irin su Kassu da Gambu."

Mamman Shata ya rike mukaman siyasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a jamhuriya ta uku, aka zabi marigayi Mamman Shata a matsayin shugaban karamar hukumar Funtua a karkashin jam'iyyar SDP.

Sai dai, an ce bai jima a kan kujerar ba, akatsige shi, sakamakon halayyarsa ta adawa, inda aka maye gurbinsa da Manjo Janar Shehu Musa Yar'adua (mai ritaya).

Ko a shekarar 1970, an ce Shata ya lashe kujerar kansila a karamar hukumar Kankia a jihar Kaduna, sannan a shekarun 1980 ya shiga jam'iyyar GNPP, kafin daga baya ya koma NPN mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.