Gwamnonin Arewa Sun Yi Magana da Murya 1 kan Rashin Tsaro bayan Taro a Kaduna
- Gwamnonin jihohin Arewa sun nuna damuwarsu kan matsalar rashin tsaron da take ƙara taɓarɓarewa a wasu garuruwa da ke yankin
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya buƙaci a sake dabarun da ake amfani da su
- Gwamnonin sun kuma nuna alhini tare da yin ta'aziyya ga mutanen jihohin yankin waɗanda hare-haren ƴan ta'adda suka ritsa da su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnonin jihohin Arewa na ƙungiyar gwamnonin Arewa (NSGF) sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da tsaro a Najeriya.
Gwamnonin na Arewa sun kuma bayyana damuwa kan koma bayan da aka samu kwana-kwanan nan a yunƙurin yaki da rashin tsaro da wasu miyagun laifuffuka.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana hakan a taron haɗin guiwa tsakanin NGSF da majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamonin Arewa sun yi taro a Kaduna
Ya bayyana cewa wannan taro ya zo a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci a tarihin yankin Arewa, inda ƙalubale da dama ke fuskantar su, wanda ke buƙatar hikima da haɗin gwiwa mai ƙarfi domin fuskantarsu.
Gwamnonin sun nuna damuwa kan sake dawowar ta'adin Boko Haram a wasu sassan Arewa maso Gabas da kuma ƙashe-kashe a Arewa ta Tsakiya.
Sun kuma buƙaci a sake duba dabarun tsaro tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Gwamnonin sun miƙa ta'aziyyarsu ga gwamnatoci da al’ummomin jihohin Plateau, Bauchi, Benue, Borno da Yobe da kuma dukkan mutanen Arewa bisa munanan kisan da aka yi a baya-bayan nan.
Me gwamnonin Arewa suka ce kan rashin tsaro?
Sun ce wannan mummunan hali na tashin hankali da kisan gilla da ake yi wa fararen hula masu zaman lafiya yana nuna gaggawar buƙatar ƙarfafa matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Asali: Facebook
"Duk da muna yabawa shugaban ƙasa bisa jajircewarsa wajen inganta tsaron ƙasa, dole ne mu amince cewa akwai koma baya a ƙoƙarin da muke yi na yaƙar rashin tsaro da wasu miyagun laifuka.”
"Dawowar ayyukan Boko Haram a Arewa maso Gabas da kuma kashe-kashe a Arewa ta Tsakiya suna buƙatar gaggawar sake duba dabarun tsaro da ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro na gwamnati daban-daban."
- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya
Tun da farko a nasa jawabin, Gwamna Uba Sani na Kaduna ya bayyana cewa halartar wannan taro alama ce ta himma da ƙudurinsu na tabbatar da cigaba da bunƙasar yankin Arewa.
Sojoji sun kashe ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ragrgazar ƴan ta'adda a jihar Katsina.
Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa bayan sun farmake su a sansaninsu da ke cikin daji.
Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ƙwato makamai masu yawa da kayayyakin da ƴan ta'addan suke amfani da su bayan sun lalata sansaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng