'Yan APC Sun Taso Gwamna Sule a Gaba kan Shugaba Tinubu
- Kalaman da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi kan tsohuwar jam'iyyar CPC ba su yi wa wata kungiya a APC daɗi ba
- Ƙungiyar wacce ta fito daga yankin Arewa ta Tsakiya ta buƙaci gwamnan ya bayyana matsayarsa kan gwamnatin Tinubu
- Ta nuna cewa lokaci ya yi da zai gayawa duniya yana tare da gwamnatin shugaban ƙasan ne ko akasin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Wata ƙungiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC daga yankin Arewa ta Tsakiya ta yi raddi ga gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Sule da ya haɗa kansa da sauran shugabannin jam’iyyar APC masu goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma yiwuwar sake tsayawa takararsa a 2027.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƙungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugabanta, Saleh Mamman Zazzaga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan APC sun yi kira ga Gwamna Sule
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Sule da ya fito fili ya bayyana matsayinsa game da gwamnatin Tinubu, musamman duba da wasu kalamai da ya yi a kwanan nan dangane da tsohuwar jam’iyyar CPC da ke cikin APC.
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan kalaman Gwamna Sule, tana mai fassara su a matsayin masu saɓani da matsayar ɓangaren CPC na goyon bayan Shugaba Tinubu.
Kungiyar ta bayyana cewa shugabancin Tanko Al-Makura na ɓangaren CPC, da ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, ya nuna ƙarara inda suka dosa a siyasance.
Ta jaddada muhimmancin rawar da Al-Makura ya taka a matsayin gwamna ɗaya tilo da aka zaɓa ƙarƙashin tutar CPC, wanda hakan ya taimaka wajen kafuwar jam’iyyar APC.
“Ba wanda zai ce ya fi Alhaji Tanko Al-Makura kasancewa ɗan CPC. A tarihi, Al-Makura ne kadai ya zama gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC, wanda hakan ya ba jam’iyyar ƙarfi a tattaunawar da ta haifar da kafa APC."
- Saleh Mamman Zazzaga
Wace buƙata aka nema wajen Gwamna Sule
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Sule da ya daina faɗin ra’ayinsa a bainar jama’a dangane da alƙiblar siyasa ta ɓangaren CPC, tana mai cewa furucin Al-Makura na goyon bayan Tinubu ya isa ya wakilci matsayar ƴan CPC.

Asali: Facebook
“Muna buƙatar Gwamna Abdullahi Sule da ya fito fili ya bayyana matsayarsa, ko yana tare da Shugaba Bola Tinubu ko kuma akasin haka."
"Idan yana tare da shugaban ƙasa, ya kamata ya haɗa kai da sauran masu kishin ci gaban gwamnatinsa domin samun nasara da kuma sake tsayawa takara a 2027."
- Saleh Mamman Zazzaga
Gwamna Sule ya magantu kan kama sana'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan kama sana'a bayan ya gama mulki.
Gwamna Sule ya bayyana cewa idan ya sauka mulki a shekarar 2027, zai koma sana'arsa ta asali watau walda.
Abdullahi Sule ya nuna cewa tun da farko ya samu ƙwarewa sosai.a fannin sana'ar walda kuma ya ci abinci da ita.
Asali: Legit.ng