Ganduje Ya Tabo Batun Maida Najeriya karkashin Jam'iyya 1, Ya Fadi Shirin APC

Ganduje Ya Tabo Batun Maida Najeriya karkashin Jam'iyya 1, Ya Fadi Shirin APC

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya kwantar da hankalin masu fargaba game da maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya mai mulki
  • Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa tara jam'iyyu da yawa a ƙasa, na kawo naƙasu wajen samar da ingantaccen shugabanci
  • Shugaban na APC ya nuna cewa idan ƴan Najeriya na son jam'iyya ɗaya ta yi ta rike madafan iko, to ba za su yi jayayya da hakan ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani kan fargabar da shugabannin jam’iyyun adawa suke yi kan cewa ana ƙoƙarin maida Najeriya ƙasa mai jam’iyya daya.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa bai kamata a yi adawa da hakan ba idan har shi ne abin da ƴan Najeriya suke so.

Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya ce ba aibu ba ne yin jam'iyya daya a kasa Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na APC dai ya jagoranci wasu sanatoci uku na PDP da ake cewa sun amince da shirin komawa jam’iyyar APC domin ganawa da Shugaba Tinubu.

Me Ganduje ya ce kan yin jam'iyya ɗaya?

Ganduje ya ce babu dalilin da zai sa APC ta yi jayayya da ƴan Najeriya idan jam’iyyar ke da iko a kusan dukkan jihohi da kuma gwamnati ta tarayya, rahoton Leadership ya tabbatar.

"Shugabanni sun damu kan jam'iyya ɗaya ƙasa. Idan kasancewar jam’iyya ɗaya a ƙasa shi ne burin ƴan Najeriya kuma abin alheri a gare su, yin jam’iyya ɗaya bai zuwa da tilas, sai da tattaunawa, kuma sai sauran jam’iyyun siyasa sun fahimci tasirin kyakkyawan mulki da jam’iyyarmu ke yi."

"Idan suka yanke shawarar komawa jam’iyyarmu da son ransu, ina ganin babu laifi a hakan."
“A yau ƙasar China na ɗaga cikin ƙasashe mafi karfi a duniya, kuma tana tafiya da tsarin jam’iyya ɗaya. Ba wai muna ƙoƙarin kafa jam’iyya ɗaya ba ne, amma idan wannan ne zabin ƴan Najeriya, ba za mu yi jayayya da su ba.
“Ka san dai ana cewa masu dafa girki da yawa suna iya lalata miya, haka nan jam’iyyun siyasa da yawa na iya lalata mulki.”

- Abdullahi Umar Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya ce jam'iyyu da yawa na lalata shugabanci Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Batun komawar sanatocin PDP zuwa APC

Da yake magana kan sauya sheƙar ƴan siyasa da ziyarar da sanatocin PDP suka kai wa Shugaba Tinubu, sai ya ka da baki ya ce:

“Wannan wani ɓangare ne na ci gaba da kokarin da Shugaba Tinubu ke yi cewa dole ne APC ta yi duk abin da ya dace ta fuskar dimokuradiyya domin ƙara yawan mambobinta."
“Kuma a wannan lokaci ba wai kawai yawan mambobi ba, har da inganci da ƙwarewar mabiyanmu.”

“A wannan batu na musamman da ya shafi jihar Kebbi, an gudanar da tattaunawa da dama a bayan fage."
"Tattaunawa da shawarwari sun gudana tsakanin manyan jiga-jigan siyasa na jihar, kuma yanzu sun yanke hukuncin cewa sakamakon hakan, sanatoci uku daga PDP na Kebbi sun amince kuma sun yanke shawarar komawa babbar jam’iyyarmu, APC."

Malami a Izala ya fice daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban malamai a Izala kuma ɗan siyasa a jihar Bauchi, Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi Kantana ya fice daga jam'iyyar APC.

Malamin addinin musuluncin ya sanar da haka ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban jam'iyyar na mazaɓar Dull.

Ya bayyana cewa ya yanke wannan hukuncin ne saboda sabon muƙamin da ya samu na shugaban majalisar malamai ta Izala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng