"Burinmu Jama'a Su Ji Daɗi," Minista Ya Jero Ayyukan Alherin Tinubu a Shekara 2
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yabi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa ayyukan alherin da yake wa al'umma tun da ya hau mulki
- Wike ya bayyana cewa makaho ne kaɗai zai ce Shugaba Tinubu ba ya aiki a Abuja amma an samu canji tun daga 29 ga watan Mayu, 2023
- Tsohon gwamnan ya ce yana fatan za a kaddamar da ayyuka da dama a bikin cikar Shugaban kasa, Bola Tinubu shekaru biyu a kan mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa an samu canji a ɓangaren gine-ginen ababen more rayuwa a Abuja.
Wike ya ce tun da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗare kan mulki a watan Mayu, 2023, ƴan Najeriya suka fara ganin canji a fannonin rayuwa daban-daban.

Asali: Twitter
Ministan ya jinjina wa Shugaba Bola Tinubu bisa samar da "ingantaccen ci gaba da sababbin tituna da gine-gine" a babban birnin ƙasar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar duba ayyuka da dama da ake ci gaba da gudanarwa a fadin Abuja, rahoton The Nation.
Bola Tinubu ya kawo ci gaba a shekaru 2
Wike ya ce sai makaho ne kawai zai ce Shugaba Tinubu bai yi komai a Abuja ba, yana mai cewa an tanadi ayyuka da dama da za a kaddamar a bikin cika shekaru biyu da hawa mulki.
"Shugaban ƙasa ya samar da ababen more rayuwa na gaske a Abuja. Kowa ya shaida cewa Abuja ta canza. Muna farin ciki da hakan.
"Ina ƙara gode wa Allah da ya ba Shugaban ƙasa damar kafa jagoranci na gari wanda ya sa mazauna Abuja ke cin moriyar dimokuraɗiyya."
“Ban ga dalilin da zai sa wani ya ce shugaban ƙasa ba ya komai ba, sai dai idan mutum makaho ne ko kuma ba ya ƙaunar gaskiya duk da abin da yake gani da idonsa.”
- Nyesom Wike.

Asali: Twitter
Ana shirin kaddamar da ayyuka a Abuja
Ya ƙara da cewa ana sa ran za a kaddamar da muhimman ayyuka kamar titin Gishiri Interchange, titin OSEX zuwa Wassa Junction, da gyara ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da sauransu.
Wike ya ce yana sa ran kaddamar da yawancin wadannan ayyuka cikin mako biyu, domin su dace da bikin cika shekaru biyu da shugaban ƙasa ya shiga ofis.
"Muna farin ciki idan mutane su na jin daɗi saboda dama muna aiki ne domin al’umma," in ji Wike.
Wike ya yi takaicin abin da aka yi wa matar Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya nuna damuwa kan fitar wasu mata daga wurin taron da uwargidan shugaban ƙasa ta halarta a Ribas.
An ruwaito cewa mata sun watse a wajen taron da uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta shirya a jihar domin nuna adawa da dakatar da gwamna Simi Fubara.
A cewar Wike, rashin girmama duk wanda ke wakiltar Uwargidar Shugaban Kasa tamkar cin mutuncin ofishin shugaban kasa ne gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng