Abbas Tajudeen: Shugaban Majalisar Wakilai Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa
- An shiga jimami bayan mutuwa ta ratsa iyalan shugaban majalisar wakilan Najeriya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen
- Surukar shugaban majalisar wakilan ta yi bankwana da duniya tana da shekara 85 a daren ranar Alhamis
- Abbas Tajudeen ya samu halartar jana'izar marigayiyar tare da sauran wasu manyan ƴan majalisar wakilai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya yi babban rashi, inda ɗaya daga cikin surukansa, Hajiya Rahmatu Bello Mukaddas, ta rasu.
Surukar shugaban majalisar wakilan ta rasu ne a daren ranar Alhamis, tana da shekaru 85 a duniya.

Asali: Twitter
Shugaban majalisar wakilan ya sanar da rasuwar mahaifiyar matar ta sa ne a shafinsa na X a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Surukar Abbas Tajudeen ta gida mu gidan gaskiya
Ya bayyana cewa Hajiya Rahmatu ita ce mahaifiyar Hajiya Hussaina, matar farko ta Rt. Hon. Abbas Tajudeen.
An yi jana’izarta a maƙabartar Tukur-Tukur da ke Zariya bayan sallar Juma’a a ranar Juma’a, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya halarci jana’izar tare da manyan ƴan majalisar wakilai ciki har da mai tsawatarwa na majalisa, Hon. Usman Bello Kumo, da mataimakin mai tsawatarwa, Hon. Ali Isa.
Haka kuma, wasu dagatai daga masarautar Zazzau da malaman addini da wasu manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun halarci jana’izar.
Shugaban majalisar ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai halaye na kirki da na ƙwarai, uwa ga kowa da rayuwarta ta kasance cike da taimako, kulawa, da sadaukar da kai.
"Na shiga cikin baƙin ciki matuƙa da rasuwar uwarmu, Hajiya Rahmatu Bello Mukaddas. Ba kawai suruka ba ce a gare ni, uwa ce ta gaskiya da ta kasance ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai a cikin iyali da al’umma."
"Rayuwarta cike take da ibada da nuna ƙauna da haƙuri ga kowa. Ta kasance mace mai yawan yafiya da taimako, kuma rayuwarta abin koyi nc ga kowa."
- Abbas Tajudeen

Asali: Twitter
Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya yi addu'o'i
A ƙarshe, shugaban majalisar ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya jikan marigayiyar, Ya sanya ta cikin rahamarsa, Ya kuma bai wa danginta haƙuri da juriyar rashin da suka yi.
Rasuwar marigayiyar ta girgiza dangi, abokai da sauran ƴan uwa, musamman ganin irin matsayin da take da shi a cikin gida da kuma al’umma gaba ɗaya.
Ta kasance uwa ce ga mutane da dama, ba kawai ga ƴaƴanta ba, har ma ga duk wanda ya kusance ta.
Tsohon mataimakin gwamna ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Delta, Farfesa Amos Utuama ya yi bankwana da duniya.
Marigayin ya kuma kasance , ya kasance kwamishinan shari’a kuma Antoni Janar na jihar Delta a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Gwamna James Ibori.
Kafin Farfesa Utuama ya tsunduma cikin harkokin siyasa, ya kasance babban malami a tsangayar shari'a ta jami'ar Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng