Mai Mala Buni
Rigingimun cikin gida sun barke wajen tantance rajistar ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC a Jihohi. Akwai wuraren da mummunan rikici ya kaure a dalilin wannan rajista.
A yau ne tsohon Shugaban Jam’iyya ya dura kan Gwamna Mai Mala Buni. Bisi Akande ya yi kaca-kaca da sabunta rajistar Jam’iyyar APC da ake yi, ya ce asara ce.
‘Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a karamar hukumar Geidam. An sace Hakimin Maganna da ke karkashin masarautar Ngazargamu a dalilin wannan mummunan hari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa a cikin sirri tare da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da kuma takwaransa na Yobe, Mai Mala Buni a Villa.
A jiya ne aka shawo kan Muhammadu Buhari ya yi watsi da gayyatar Majalisa. Domin ana ganin cewa za ayi amfani da wannan dama ne a ci mutuncin shugaban kasar.
Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya ta jam'iyyar APC, ya shawarci sanatocin da aka zaba ta jam'iyyar APC da su yi aiki tukuru na kokarin gyarawa APC.
An samu wadanda su ke yi wa tsohon Gwamnan jihar Zamfara yakin zama Shugaban APC. Suna ganin Kudu za su fito da Shugaban kasa, Arewa ta rike Shugaban Jam’iyya.
A yayin da ya ke tayasu murnar samun mukaman, Malam Gusau ya ce mutanen da aka nada zasu bawa gwamnatin Borno gudunmawa a kokarinta na samar da jagoranci mai ma
Sanata Kabiru Marafa ya yi watsi da jinkirin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wajen gudanar da babban taro na zabar shugabannin jam’iyyar.
Mai Mala Buni
Samu kari