Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni

Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni

- An rurowa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe wuta a kan gudanar da babban taron APC na kasa

- Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun matsu su ga an zabi sabbin shugabannin jam’iyyar

- Harma, Sanata Kabiru Marafa ya ba Buni zuwa Disamba 2020 ya gudanar da taron ko kuma ya yi murabus daga matsayin shugaban jam’iyyar

Sanata Kabiru Marafa ya yi Alla-wadai da jinkirin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wajen gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.

Da yake magana a ranar Lahadi, Marafa ya koka a kan hukuncin kwamitin rikon kwarya na Gwamna Mai Mala Buni na Yobe da ya fara rijistan mambobi kafin taron, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanatan ya yi ikirarin cewa wannan yunkurin ya saba ma kundin tsari kuma wani makirci ne na Buni domin ya tsawaita mulkinsa a matsayin Shugaban jam’iyyar.

Bugu da kari, jigon na APC ya bayyana cewa bisa ga kundin tsari, bai kamata ace Buni ne a kan harkoki ba, amma cewa shi da sauran jiga-jigan jam’iyyar sun yi shiru saboda Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Kariya zamu bata: Dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ta gayyaci Rahama Sadau

Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni
Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni Hoto: Neptune Prime/Today.ng
Asali: UGC

“Da dama daga cikinmu sun san cewa nadinka baya bisa kundin tsari, [sashi 17(iv) na kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu a bayyane yake karara]. Kawai dai mun yi shiru ne saboda mutuncin Shugaban kasar da muke gani, da kuma yardar cewa jam’iyyar na bukatar bude sabon shafi.”

Marafa ya ci gaba da fadin cewa an ba Buni zuwa Disamba 2020 ya gudanar da wani babban taro da zai sa a zabi sabbin shugabanni ko kuma ya yi murabus.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Babban kantin uwar gidan Ajimobi ya kama da wuta a Ibadan

Ya kara da cewa:

“Ka kwana da sanin cewa za a soke duk wani mataki da za ka dauka wanda ya saba hakkinka na shirya taron al’ada da zai bayar da damar zabar sabbin shugabanni kuma ba zai yi tasiri ba. Kana da daga yanzu zuwa Disamba doming a aiwatar da abunda ya kamata ko mu fatattake ka.

“Jiharka na bukatarka fiye da jam’iyyar, ka je ka kula jiharka, ba zai yiwu ka kasance Gwamna kuma Shugaban APC ba a lokaci guda. Ya saba kundin tsari.”

A baya mun ji cewa, Kabiru Marafa, tsohon daga Zamfara ta tsakiya, ya zargi gwamna Mai Mala Buni, mai kula da kwamitin sulhun jam'iyyar APC, da shararo zuƙi ta malle.

A cewar Marafa, batun sulhunta rikicin jam'iyyar a jihar Zamfara duk shifcin gizo ne, ba gaskiya bane kamar, yadda kwamitin ke da'awar ya sulhunta komai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel