Rigingimun cikin gida sun bi sun dabaibaye APC wajen tantance rajistar ‘yan Jam’iyya a Jihohi

Rigingimun cikin gida sun bi sun dabaibaye APC wajen tantance rajistar ‘yan Jam’iyya a Jihohi

- Ana samun matsala wajen yi wa ‘Ya ‘yan Jam’iyya rajista a wasu Jihohi

- Akwai wuraren da mummunan rikici ya kaure a dalilin wannan rajistar

- A irinsu Kwara, Delta da Osun, abubuwa ba su tafiya yadda su ka kamata

Aikin yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC rajista ya zama abin da ya zama. Jaridar The Nation ta ce rikici sun barke a wasu jihohi a dalilin wannan aiki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin inda lamarin ya yi kamari akwai jihohin Delta, Osun da Kwara.

A jihar Delta, Sanusi Musa, wanda aka ba nauyin wannan aiki ya yi murabus, da ya ke bayani, ua ce ya samu kansa a wani irin yanayi da ya sa ya bar aikin.

Sakataren riko na jam’iyyar APC na kasa, Chidi Okonji, ya zargi shugaban aikin rajista na jihar Delta, Wilson Anyaegbu, da nuna son kai wajen yin rajistan.

KU KARANTA: Za ayi wa 'Yan APC sulhu a Jihar Delta

Chidi Okonji ya ce an ware manyan APC irinsu Festus Keyamo; Victor Ochei; O’tega Emerhor, da Cif Great Ogboru, a rajistar da ake yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar.

Tuni dai Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo SAN, ya rubuta takarda zuwa ga Mai Mala Buni, Ovie Omo-Agege, da wasu manyan APC, ya na korafi.

A jihar Kwara kuwa, magoya bayan tsohon shugaban jam’iyya wanda aka dakatar, Bashir Bolarinwa, sun yi watsi da wannan aiki na rajista da ake yi.

Jagoran APC a Kwara, Sunday Odebiyi, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an maida su saniyar ware.

Mala Buni
Shugaban riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: APC: An yi wa Shugaban jam'iyya da magoya bayansa duka a Kwara

A jihar Osun ma an samu matsala, inda ake kukan ba a kai kayan aiki a wasu wurare ba. A jihohi irinsu Akwa Ibom, Nasarawa, Gombe, abubuwa na tafiya sumul.

A Ebonyi kuwa, gwamna David Umahi ya bukaci a kara masu fam domin APC ta na kara farin-jini.

A baya kun ji cewa aikin rajistar ya na fito da sabanin da ke cikin gidan APC baro-baro, inda wasu ke ganin cewa babu inda doka ta ce a tantance ‘ya ‘yan jam’iyya.

Irinsu Adams Oshiomhole sun ce rajistar APC da ake yi ta saba doka. Tsohon shugaban na APC na kasa ya ce ya yi rajista ne kawai saboda a zauna lafiya a jam’iyya.

Wannan shi ne ra'ayin Bola Tinubu, da na-hannun damansa kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa na farko, Olabisi Akande, akasin ra’ayin magajinsa, John Oyegun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel