EndSARS: APC ta zayyana buƙatunta ga Buhari kan masu zanga-zanga

EndSARS: APC ta zayyana buƙatunta ga Buhari kan masu zanga-zanga

- APC ta yaba ma Shugaba Buhari kan kokarinsa wajen dawo da zaman lafiya a Najeriya sakamakon zanga-zangar EndSARS

- Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta tallafa wa shugaban kasar wajen aiwatar da bukatun masu zanga-zangar

- Mai Mala Buni, shugaban kwanitin rikon kwarya na APC na kasa, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba

Sakamakon zanga-zangar EndSARS da ke gudana a kusan dakkanin jihohin kasar, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bukaci matasa da su janye gangaminsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar ta ce za ta tallafa wa shugaban kasa Muhammdu Buhari wajen aiwatar da bukatun masu zanga-zanga don ganin zaman lafiya da hadin kai ya dawo a kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa a wani jawabi a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban APC na kasa, Mai Mala Buni, ya yi tsokaci kan batun.

KU KARANTA KUMA: Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu

Ya ce jam’iyyar ta yi maraba da hukuncin yin gagarumin sauye-sauye, ciki harda duba albashin yan sanda kamar yadda Shugaba Buhari ya sanar.

EndSARS: APC ta zayyana buƙatunta ga Buhari kan masu zanga-zanga
EndSARS: APC ta zayyana buƙatunta ga Buhari kan masu zanga-zanga Hoto: @dailt_trust
Asali: Twitter

Ya yi kira ga yan Najeriya da kada su siyasantar da zanga-zangar EndSARS don cimma wata manufar siyasa, inda ya kara da cewar rikici na bukatar sulhu don amfanin kasar.

Gwamna Buni ya ce:

“Ga matasanmu, an samu sakonku kuma an fahimce ku sosai. Mataki na gaba da ya zama dole a bi shine bukatar tattauna da dukkanin tsare-tseren gwamnati domin magance dukkanin damuwar da ke kewaye da zanga-zangar da tasirin gwamnati gaba daya.”

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

A gefe guda, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) ta bada sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa kayayayyakin da aka kwashe daga ma'adanarta a yankin Narayi sun hada da magunguna masu tarin hatsari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel