Isra'ila Za Ta Shiga Uku, Iran Ta Yi Mata Gagarumar Barazana game da Lebanon

Isra'ila Za Ta Shiga Uku, Iran Ta Yi Mata Gagarumar Barazana game da Lebanon

  • Sojojin Iran sun yi barazanar mayar da martani mai tsanani ga Isra'ila game da kai hare-haren a kudancin Lebanon
  • Iran ta ce Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 84 tun bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka
  • Hare-haren Isra'ila a kudancin Lebanon sun kashe mutum hudu duk da yarjejeniyar da aka ce ta kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi barazanar mayar da martani mai tsanani kan Isra'ila.

Ƙasar ta yi barazanar ce bayan hare-haren da aka kai a kudancin Lebanon da suka kashe mutum hudu.

Iran ta yi barazana ga Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Marc Israel SELLEM/POOL/AFP, Foad Ashtari/SOPA Images/LightRocket.
Source: Getty Images

Rahoton Al Jazeera ya ce an kai harin ne duk da yarjejeniyar da Tehran da Washington suka cimma wanda wasu ke ganin zai kawo karshen yakin da ake yi.

Kara karanta wannan

Sulhu tsakanin Iran da Amurka ya fusata Isra'ilawa, sun dura kan Netanyahu

Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amurka, Iran

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya, ciki har da rikicin Lebanon.

Babban rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta bayyana cewa idan sojojin gwamnati masu kashe yara ba su kawo karshen hare-harensu a kudancin Lebanon ba, to su jira martani mai tsauri daga rundunonin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Sanarwar ta kara da cewa Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon sau 84 tun bayan sanar da cimma yarjejeniyar tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

Sanarwar ta ce:

""Ya kamata Isra'ila ta yi tsammanin fuskantar kakkausar martani idan ta ci gaba da aikata miyagun laifuffuka tare da yi wa al'ummar Lebanon da ake zalunta kisan kiyashi."
Netanyahu ya sha alwashi game da kai hari a Lebanon
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Alwashin Isra'ila game da farmaki a Lebanon

Rahoton ya ce wannan barazana ta Iran na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin tabbatar da dorewar yarjejeniyar zaman lafiya bayan rikicin da ya addabi yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Iran ta fara samun tagomashi daga Turai bayan tsayar da yaki da Amurka

Rahotannin da ke da alaka da batun sun hada da batun rattaba hannu kan yarjejeniyar Amurka da Iran a Switzerland da kuma kalaman Shugaba Donald Trump cewa Tehran ba za ta mallaki makaman nukiliya ba.

Haka kuma, an ruwaito cewa jiragen dakon danyen man Iran sun koma gudanar da jigila bayan yarjejeniyar da Amurka duk da cewa Isra'ila na jan kafa game da sulhun.

Har ila yau, jakadan Isra'ila ya ce kasarsa ba za ta janye daga matakanta a Lebanon ba kuma ba za ta aikata abin da ya kira kashe kanta ba.

Sulhu: Isra'ilawa sun dura kan Netanyahu

Mun ba ku labarin cewa Isra’ilawa daga bangarori daban-daban sun nuna fushi kan yarjejeniyar farko tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan ƙasar suna kallonta a matsayin barazana ga tsaron Isra’ila yayin da ake tsaka da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Firayim ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce zai ci gaba da hana Iran mallakar makamin nukiliya, ko da yarjejeniya ta tabbata ko ta rushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.