Buni ga Sanatocin APC: Ku zage damtse, nasara tamu ce a kodayaushe

Buni ga Sanatocin APC: Ku zage damtse, nasara tamu ce a kodayaushe

- Mai Mala Buni, Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, ya gabatar wa da sanatoci wani jawabi na musamman

- A cewarsa, ya kamata wadanda jam'iyya ta zaba su yi iyakar kokarinsu wurin dawowa da APC sunanta don ta cigaba da mulki

- A cewarsa, akwai tsari daban-daban da ya kamata a samar musamman batun rijista, wasu sun shiga jam'iyyar kuma ba a saka sunayensu ba

Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya ta jam'iyyar APC, ya shawarci sanatocin da aka zaba ta jam'iyyar APC da su yi aiki tukuru na kokarin gyarawa APC sunanta a idon 'yan Najeriya.

Ya fadi hakan ne a wani taro da yayi da sanatocin APC a majalisar dattawa ranar Laraba, Buni ya ce wajibi ne jam'iyya mai mulki ta samu nasara a kowanne akwatin zabe.

A cewarsa, kwamitinsa tana iyakar kokarinta na ganin jam'iyya ta ci nasara cikin tsaftatacciyar hanya, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Katsina: Masari ya dauka malaman makaranta 4,250 don inganta ilimi

Buni ga Sanatocin APC: Ku zage damtse, nasara tamu ce a kodayaushe
Buni ga Sanatocin APC: Ku zage damtse, nasara tamu ce a kodayaushe. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Kafin a hada kwamitin, sai da NEC ta rushe NWC wacce Adam Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC ya jagoranta.

Buni ya ce yanzu haka an gama shirye-shiryen fara rijistar mambobin jam'iyya.

"Inaso in bayar da shawara a matsayina na dan kungiya mai neman cigaban APC, ya kamata mu fara tunanin yadda jam'iyyarmu za ta cigaba da zama a kujerar mulki ba daya, biyu, uku ko kuma hudu ba," cewarsa.

KU KARANTA: Hotunan tubabbun barayin kayan tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato

"Sai dai babban abin takaici shine yadda tun da jam'iyyar ta kafu a 2013, batada cikakken rijista a jihohi 36 dake Najeriya har da babban birnin tarayya, Abuja.

"Sannan har yanzu akwai 'yan jam'iyyar da su ka bar ta a 2018 su ka koma jam'iyyar adawa, amma har yanzu sunayensu sunanan a cikin 'yan jam'iyya.

"Sannan wadanda su ka shiga jam'iyyar tun 2014, har yanzu ba a yi rijistar sunayensu ba."

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari yankin Yolde pete da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Mazauna yankin tare da jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, miyagun dauke da makamai sun tsinkayi gidan dansanda makusancin Atiku Abubakar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, an gano cewa 'yan bindigan sun so tarar da dan sandan ne bayan sun zargi sun iso gari tare da Atiku Abubakar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng