Abin Tausayi: Bayan Daura Aure, Amarya Ta Dauki Wuka Ta Yanka Wuyan Angonta a Kano
- Ana zargin wata amarya da ba a wuce watanni biyu da aurenta ba, ta kashe mijinta a unguwar Rimin Kebe da ke Jihar Kano
- Ganau da lamarin ya auku a kan idonsu sun ce matar ta yanka makogwaron angonta yayin da sabanin ya shiga tsakaninsu
- Dakarun rundunar ’yan sanda sun garzaya wurin bayan samun rahoto, kuma an ce sun kama matar da ake zargi domin ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ana zargin wata amarya da ba a dade da daura aurenta ba, mai suna Fatima da kashe angonta, Auwalu, bayan ta daba masa wuka a wuya a unguwar Rimin Kebe da ke Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi bayan wata gardama da ta barke tsakanin ma’auratan, wadanda aka ce aurensu bai kai wata biyu ba.

Source: Original
Yadda amarya ta kashe angonta
Jadidar Aminiya ta ruwaito cewa wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa mamacin ya fito daga cikin gida yana neman taimako bayan an daba masa wuka.
A cewarsa, Auwalu ya rika ihu yana sanar da mutane cewa matarsa ce ta daba masa wuka.
“Fatima ta daba masa wuka a wuya. Ya fito yana ihu cewa matarsa ce ta caka masa wuka. Aka kai shi ofishin ’yan sanda sannan aka garzaya da shi asibiti, amma ya rasu kafin a isa,” in ji majiyar.
Majiyoyin unguwar sun ce matar ta yi ikirarin cewa ba ta son mijin nata tun farko, kuma aurensu ba a kan soyayya aka gina shi ba.

Kara karanta wannan
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Khan Salihu ya rasu bayan ya dawo daga masallaci
Ana zargin ta bayyana cewa an tilasta mata yin auren, lamarin da ake kyautata zaton ya taimaka wajen haddasa sabanin da ya kai ga wannan mummunan al’amari.
’Yan sanda sun kama amaryar
Bayan faruwar lamarin, jami’an ofishin ’yan sanda na Zango da ke yankin Ɗantamashe suka garzaya wurin da lamadin ya faru, sannan suka kama matar da ake zargi.
Majiyoyi sun tabbatar cewa tana tsare a hannun ’yan sanda yayin da ake gudanar da bincike kan abin da ya faru.

Source: Facebook
’Yan sanda sun yi gum da bakinsu
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba.
Rahotanni sun ce bai amsa kiran waya ko sakonnin da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Ana sa ran rundunar za ta fitar da cikakken bayani bayan kammala binciken farko kan lamarin.
Uwargida ta cinna wa kishiya wuta
A wani labarin, kun ji cewa wata matar aure, Maryam Muhammad, ta banka wa kishiyarta da kananan yara biyu wuta a jihar Kano.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a unguwar Mai Allo da ke Hotoro da misalin karfe 3:00 na asuba, inda kishi ya rikide ya koma tsantsar rashin tausayi.
Majiyoyi sun bayyana cewa, uwargidan ta yi amfani da fetur wajen cinna wa amaryarta da yaranta wuta, lamarin da ya tada hankulan jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

