Boko Haram: ‘Yan ta’adda sunyi ta’adi, an yi awon gaba da Mai Gari a Geidam

Boko Haram: ‘Yan ta’adda sunyi ta’adi, an yi awon gaba da Mai Gari a Geidam

-Ana zargin ‘Yan Boko Haram da kai hari a karamar hukumar Geidam

-‘Yan ta’addan sun kona gida da shaguna bayan sun saci kayan abinci

-An sace Hakimin Maganna da ke karkashin masarautar Ngazargamu

Wasu miyagun ‘yan ta’adda da ake zargin cewa ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram ne sunyi mummunar barna a kauyen Geidam da ke jihar Yobe.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis cewa wadannan ‘yan ta’adda sun fasa shagunan Bayin Allah, sun saci kayan abinci a garin.

Bayan nan ‘yan ta’addan na kungiyar Boko Haram sun kona wasu daga cikin shagunan kurmus.

Wani Bawan Allah da aka yi abin gaban idonsa, ya shaidawa jaridar haka, ya ce bayan nan an kona gidan tsohon shugaban karamar hukuma, Mulima Mato.

KU KARANTA: Kwastam ta gano makamai da aka boye cikin wasu kaya

Jami’an ‘yan sanda ta bakin Dungus Abdulkarim, sun tabbatar da aukuwar wannan ta’adi, sunce sun gano gawar wasu mutum biyu da aka kashe a kauyen.

Sannan jami’in ‘dan sandan ya tabbatar da cewa an dauke Hakimin garin Geidam. Ana zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi wannan danyen aiki.

Tuni dai mai girma gwamna Mai Mala Buni ya fito ya yi magana, yana umartar ma’aikatan bada agajin gaggawa na SEMA, su kai doki zuwa garin na Geidam.

Gwamnan jihar Yobe ya yi jawabi a jiya ta bakin mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed, ya na tir da wannan hari da aka kai wa mutanen Geidam.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: Abin da ya kora mutanen Fulani daga Ebonyi

Boko Haram: ‘Yan ta’adda sunyi ta’adi, an yi awon gaba da Mai Gari a Geidam
Tsohon Gwamna Ibrahim Geidam Hoto: Facebook Daga: Nigeria-Book-of-Records
Source: Facebook

Jaridar AljazirahNigeria ta ce iyalin Hakimin Maganna da aka dauke sun roki gwamnatin jihar Yobe ta san yadda za tayi, ta ceto da shi daga hannun miyagu.

'Yan bindiga sun kashe mutane hudu tare da yin garkuwa da mata a kauyen Katarma a Jihar Kaduna kamar yadda jami'an gwamnati suka tabbatar a jiya.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kadunaa, Samuel Aruwan ya shaidawa manema labarai cewa ce an ceto gaba daya matan nan da aka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ya ce akwai jami'an sintiri daga cikin mutanen da yan bindigar suka kashe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel