‘Ya ‘yan APC sun fara buga wa Abdulaziz Yari gangar zama Shugaban Jam’iyya

‘Ya ‘yan APC sun fara buga wa Abdulaziz Yari gangar zama Shugaban Jam’iyya

- Wasu ‘Ya ‘yan APC suna so mulkin Najeriya ya koma Kudu a zaben 2023

- Kungiyar tana ganin abin da ya dace shi ne a ba Arewa shugaban Jam’iyya

- Bashir Yusuf ya ce Abdulaziz Yari ne ya kamata a bar wa rikon Jam’iyyar

Wata kungiya ta ‘yan siyasar da suka nemi kujeru a jam’iyyar APC a 2018, suna goyon bayan shugaban kasa ya fito daga kudancin Najeriya.

Jaridar Guardian ta ce wadannan ‘ya ‘yan na APC suna son ganin magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga yankin kudu.

Bashir Muhammed Yusuf a wata hira da ya yi da ‘yan jarida da yawun bakin kungiyar tasu ya bayyana wannan jiya a birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Mai Mala Buni ya ki bayyana yankin da za a ba tikiti a 2023

Alhaji Bashir Muhammed Yusuf ya ke cewa tun da yanzu mulki na hannun ‘dan Arewa, ya kamata a zabe mai zuwa, a mika takara zuwa Kudu.

Yace: “Wannan shi ne abin da muke so, kuma shi ne ya fi dacewa da kasar nan. Hakazalika, shugaban jam’iyya zai dawo Arewa, sai a juya kujerun.”

A ra’ayin Bashir Muhammed Yusuf, babu wanda ya dace ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa illa tsohon gwamna Alhaji Abdulaziz Yari.

Kungiyar tana ganin cewa idan APC tana son samun nasara a zaben 2023, to Abdulaziz Yari ya kamata ya maye gurbin da Adams Oshiomhole ya bari.

KU KARANTA: Marafa ya huro wa Buni ya shirya zaben shugabannin APC

‘Ya ‘yan APC sun fara buga wa Abdulaziz Yari gangar zama Shugaban Jam’iyya
Abdulaziz Yari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Abdulaziz Yari ya yi gwamna har sau biyu a jihar Zamfara, sannan ya rike shugaban kungiyyar gwamnonin jam’iyyar APC a lokacin da yake ofis.

Kungiyar ta ce APC tana bukatar cikakken ‘dan jam’iyya, wanda ya san harkar siyasa, sannan ya fahimci abin da shugabanci da rike mukami ya kunsa.

Dazu kun ji cewa Minisan ayyuka da gidaje na kasa, Babatunde Fashola ya bayyana yarjejeniyar da aka yi tsakanin shugabannin APC kafin zaben 2015.

Ministan ya ke cewa APC ta yi amanna da tsarin kama-kama, don haka yankin Kudu ya kamata su fito da wanda zai zama magajin Muhammadu Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng