Buhari ya gana da Shugaban rikon kwarya na APC da gwamnan Kogi

Buhari ya gana da Shugaban rikon kwarya na APC da gwamnan Kogi

- Shugaban kasa Buhari ya sa labule tare da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da takwaransa na Yobe, Mai Mala Buni

- Manyan jiga-jigan na jam'iyyar APC mai mulki a kasar sun gana ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja

- Sai dai basu bayyana abunda ganawar tasu ta kunsa ba domin sun ki cewa uffan bayan haduwar tasu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, ya karbi bakuncin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari ya yi ganawar sirri tare da gwamnan wanda ya samu rakiyar Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Daga Gwamna Bello har Shugaban na APC sun ki amsa tambayoyi daga manema labarai bayan taron.

Buhari ya gana da Shugaban rikon kwarya na APC da gwamnan Kogi
Buhari ya gana da Shugaban rikon kwarya na APC da gwamnan Kogi Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: 2023: Yan Nigeria na jiran PDP ta karbi mulki, in ji Wike yayinda ya karbi bakuncin sanata Ndume

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babu mamaki Shugaban kasar ya yi amfani da taron wajen ba gwamnan jihar Kogi da Shugaban na APC shawara game da jam’iyyar da kuma kasar.

A makon da ya gabata ne fastocin kamfen din gwamnan na jihar Kogi ya bayyana a manyan hanyoyi a Kano gabannin zaben shugaban kasa na 2023.

An gano fastocin da ke dauke da rubutun da ke nuna kudirin gwamnan na neman shugabancin kasa a 2023, a wasu yankunan cibiyar kasuwancin na arewa.

Yayinda gwamnan bai kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa a 2023 ba, har yanzu akwai manyan hotunansa a wasu wurare a jihar Kogi inda ake bukatarsa da ya fito takarar shugaban kasa a zabe na gaba.

A wani labarin, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa yan Naeriya sun kagu don ganin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karbe mulki daga hannun All Progressives Congress (APC) a 2023 domin yin shugabanci nagari.

Wani jawabi da Kelvin Ebiri, hadimin labaran Wike ya sa hannu sannan Legit.ng ta gano a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu ya nuna cewa gwamnan na Ribas ya bayar da tabbacin ne a wajen bikin kaddamar da wani aikin gina hanya.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, shahararren sanatan APC shine ya kaddamar da aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel