Gwamnoni da Jam'iyya na da hannu wajen sa Shugaban kasa watsi da gayyatar Majalisa

Gwamnoni da Jam'iyya na da hannu wajen sa Shugaban kasa watsi da gayyatar Majalisa

-An shawo kan Muhammadu Buhari ya yi watsi da hallara gaban ‘Yan Majalisa

-Gwamnoni da manyan APC su na cikin wadanda su ka bada wannan shawara

-A nasu hangen, za ayi amfani da wannan dama ne a ci mutuncin shugaban kasa

A wajen taron gaggawa na NEC da jam’iyyar APC mai mulki ta yi, an kawo maganar zuwan shugaba Muhammadu Buhari zuwa zauren majalisa.

A baya an shirya cewa shugaban kasar zai bayyana a gaban ‘yan majalisar tarayya domin ya yi masu bayanin abin dake faruwa game da sha’anin tsaro.

Wani fitaccen gwamna daga yankin Kudu ya tasa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a gaba a kan gayyatar da suka aika wa shugaban kasa.

Wannan gwamna na APC ya nemi jin dalilin da ya sa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ba ‘yan majalisar dama cewa shugaban kasa ya bayyana a gabansu.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana ainihin makasudin rufe iyakokin Najeriya

Femi Gbajabiamila ya ce shugaban kasar ya na da damar ya hallara a zauren majalisar ko ya ki.

Jaridar Premium Times da Arise su ka ce a nan aka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya yi fatali da wannan goron gayyata na majalisa.

A gefe guda kuma, gwamnan jihar Yobe wanda shi ne shugaban rikon-kwarya na APC, Mai Mala Buni, ya ce sun cin ma matsaya a game da wannan magana.

Mai Mala Buni ya ce jam’iyya ta yarda cewa shugaban kasa ba zai bayyana gaban ‘yan majalisa ba. Wannan bai yi wa ‘yan majalisar APC da ke taron dadi ba.

KU KARANTA: Majalisa ta ki amincewa da abin da aka warewa Arewa maso gabas a 2021

Gwamnoni da Jam'iyya na da hannu wajen sa Shugaban kasa watsi da gayyatar Majalisa
Manyan APC a taro Hoto: www.bbc.com/pidgin/tori-53180988
Source: UGC

Gwamnonin jam’iyyar APC sun ce sun samu labari cewa ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP za su yi amfani da wannan dama ne su ci mutuncin shugaban kasar.

Dazu kun ji cewa wani daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC ya yi magana game da wannan batu, ya ce ba shugaban kasa ya kamata ya saurari 'yan majalisar ba.

Farouq Adamu Aliyu ya bayyana cewa bai kamata Buhari ya amsa gayyatar majalisar da kansa ba, ya ce wannan aikin manyan hafsoshin tsaron kasar ne.

Jigon na APC uma tsohon 'dan majalisar Jigawan ya ce Buhari ba mai son yawan surutu ba ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel