Wasu Mutanen Zamfara Za Su Baro wa Ministan Tsaro Aiki kan Zargin Badakalar Takardu
- Wata kungiyar fararen hula a jihar Zamfara ta ce tana shirin maka Ministan tsaro, Bello Matawalle a kotu kan takardun karatunsa
- Kungiyar ta yi zargin cewa Matawalle ya yi amfani da takardar makarantar koyon sana’a wajen samun mukaman siyasa da gwamnati
- Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Bello Matawalle bai fitar da wata sanarwa kan sababbin zarge-zargen da ake jifarsa da su ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zamfara - Wata kungiyar da ke fafutuka kan ci gaban Zamfara (ZSCC) ta bayyana shirin maka tsohon gwamnan jiharsu kuma karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, a kotu.
Kungiyar ta ce tana son kalubalantar sahihancin wasu takardun karatu da ake zargin Matawalle ya yi amfani da su wajen neman mukaman gwamnati.

Source: Twitter
Shugaban kungiyar, Barista Musa Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, ciki har da Legit.ng Hausa.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Fitacciyar mai zanen tufafin kwalliya, Sadia Sanusi ta riga mu gidan gaskiya
An dauko zancen takardun Bello Matawalle
A cewarsa, kungiyar ta kammala tuntubar lauyoyi kuma tana shirin daukar matakin shari’a domin kotu ta binciki batun takardun karatun Matawalle.
Kungiyar ta yi zargin cewa Matawalle ya yi amfani da wata takarda daga makarantar koyon sana’a ta VTC da ke Bunza wajen shiga siyasa da kuma samun mukamin minista.
Sai dai kungiyar ta ce akwai tambayoyi kan ko takardar ta cika sharuddan kundin tsarin mulkin Najeriya.
Barista Musa Abdullahi ya ce mukaman gwamnati na bukatar gaskiya da rikon amana tare da bin doka yadda ya kamata.
“Ba daidai ba ne mutum ya samu mukamin gwamnati ta hanyar bayar da bayanan karya ko amfani da takardun da ake da shakku a kansu,” in ji shi.
Kungiya ta bukaci a binciki batun
Lauyan ya kara da cewa dokokin Najeriya sun haramta yin jabun takardu da bayar da bayanan karya domin samun wani matsayi ko cin moriyar wani shiri.
Kungiyar ta bayyana cewa idan kotu ta tabbatar da cewa an yi amfani da takardun karya wajen samun mukami, hakan na iya jawo hukuncin cire mutum daga mukami da kuma gurfanar da shi a gaban doka.

Kara karanta wannan
Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga
Ta kuma ce ya kamata hukumomi su kwato albashi, alawus da sauran anfani da aka samu idan aka tabbatar da samun mukami ta hanyar karya.
Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin daukar mataki kan irin wadannan zarge-zarge na iya rage amincewar jama’a ga shugabanci da tsarin dimokuradiyya.

Source: Original
Matawalle: Kungiya za ta tauna tsakuwa
Haka kuma ta soki wasu kalaman Matawalle kan matsalar tsaro, tana mai cewa ya kamata shugabanni su rika bayar da bayanan da za su kwantar wa jama’a hankali.
Barista Musa Abdullahi ya ce shirin kai karar ba wai wani tuggu ne kan mutum daya ba, illa dai kare mutuncin mukaman gwamnati da tabbatar da cewa gaskiya ta kasance ginshikin shugabanci.
Ya ce matakin zai zama gargadi ga duk wanda ke tunanin amfani da bayanan karya domin samun mukami.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Bello Mohammed Matawalle bai fito fili ya mayar da martani kan sabbin zarge-zargen ba.
Ana so Tinubu ya tsige Matawalle
A wani labari mun ruwaito cewa, Bello Matawalle, Karamin ministan tsaro, na fuskantar suka daga jama'a, inda aka yi ta kiraye-kiraye ga Shugaba Bola Tinubu da ya tsige shi.

Kara karanta wannan
Rahoto: Dalilin da ya sa Atiku ya 'zabi' Amaechi a matsayin abokin takararsa a 2027
Zarge-zargen da ake yi wa Matawalle sun fi mayar da hankali kan zamaninsa na gwamnan jihar Zamfara da kuma rashin iya ba da gudummawa mai ma’ana ga tsarin tsaron Najeriya.
Kungiyoyi da dama sun zarge shi da yin almubazzaranci da kuɗin jama’a da kuma gaza magance ‘yan fashi a jihar, wadda ya har yanzu ta'addanci ya ki karewa a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng