Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki

Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki

- Diyar Sani Abacha, Gumsu Abacha ta auri Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni

- An yi bikin auren ne a gidan Mohammed Abacha a babban birnin tarayya, Abuja

- A wannan makon ne Maryam Abacha ta cika shekaru 73 a duniya

Bayan kwanaki kadan da aurar da diyarta, Gumsu Abacha, a bikin da ba a yi wani babban shagali ba ga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, matar tsohon shugaban kasar Najeriya ta shiga shagali.

Maryam Abacha ta kasance mace mai kamar maza sakamakon tsayawa yaranta da tayi bayan rasuwar mijinta, tsohon shugaban kasa na mulkin soji a shekaru masu yawa da suka gabata.

Wannan lokaci ne na shagalin murna ga dukkan iyalan. A makon da ya gabata ne aka yi bikin auren Gumsu a gidan Mohammed Abacha dake Abuja.

A ranar Alhamis, Maryam Abacha ta yi shagalin cikarta shekaru 73 a duniya.

KU KARANTA: Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya

Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki
Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki. Hoto daga thisdaylive.com
Asali: UGC

Duk da Gumsu ta taba auren biloniyan kasar Kamaru, Bayero Fadil Mohamadou, tuni dai suka rabu, The Nation ta wallafa.

Yanzu haka ita ce mata ta hudu ga Gwamna Buni, wanda ya auri diyar wanda ya gada, Ummi Adama Gaidam a kwanakn baya.

Allah ya albarkaceta da 'ya'ya 10, 3 mata da maza 7, Maryam Abacha ce matar shugaban kasan najeriya daga 1993 zuwa 1998 lokacin da ya rasu.

KU KARANTA: Mutum 101 da ake zargin 'yan Boko Haram ne suna maka FG a kotu, sun bukaci diyyar N303m

A wani labari na daban, nan babu dadewa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed zai koma jam'iyyar APC, cewar gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.

Gwamna Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin bikin saka harsashin sabon gagarumin gidan gwamnatin jihar Bauchi da zai lamushe N6.3 biliyan, Channels TV ta wallafa.

"Bari in sake nuna godiyata ga takwarana gwamnan jihar Bauchi da sauran takwarorina na arewa maso yamma da suke bani goyon baya mai matukar yawa."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel