Labari Da Ɗuminsa: Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Ihejirika, ya shiga APC

Labari Da Ɗuminsa: Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Ihejirika, ya shiga APC

- Janar Oyeabo Ihejirika, tsohon babban hafsan sojojin kasa na Nigeria ya shiga jam'iyyar APC

- Mamman Mohammed, mai magana da yawun shugaban riko na APC, Mai Mala Buni ne ya sana da hakan

- Mohammed ya ce Mai Mala Buni ya yi maraba da Ihejirika ya kuma ce shigowarsa APC zai kara wa jam'iyyar karsashi a Kudu maso Gabas baki daya

Tsohon babban hafsan sojojin kasa na Nigeria, Janar Oyeabo Ihejirika ya shiga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a ƙasa, Vanguard ta ruwaito.

Alhaji Mamman Mohammed, Direktan Watsa Labarai na Gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin riko da daidaito na APC, ne ya bada sanarwar hakan a ranar Juma'a a Abuja.

DUBA WANNAN: A Karo na Biyu, Masu Garkuwa Sun Sace Jigon APC a Lokacin Da Ya Tafi Duba Gonarsa

Labari Da Ɗuminsa: Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Ihejirika, ya shiga APC
Labari Da Ɗuminsa: Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Ihejirika, ya shiga APC. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Mohammed ya ce Buni, wanda kuma shine gwamnan jihar Yobe ya tarbi tsohon shugaban sojin zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

"Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru da Shugaban Kwamitin Tsare-tsare da tuntuba na APC, Farouk Aliyu ne suka gabatar da Ihejirika ga shugaban jam'iyyar a hukumance," in ji shi.

Ya bayyana cewa ya jiyo Buni na cewa, "Shigowar Janar Ihejirika zuwa APC zai ƙara wa jam'iyyar karsashi a Abia da yankin Kudu maso Gabas baki ɗaya.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

"Wannan muhimmin lokaci ne a jam'iyyar mu a yayin da Janar Ihejirika da wasu ƴaƴan yankin ke shigowa jam'iyyar mu domin su matso da yankin Kudu maso Gabas zuwa tsakiya domin a tafi tare."

Ya ƙara da cewa jam'iyyar na fatan samun mutane daga yankin Kudu maso Gabas da za su shigo cikinta.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel