Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock

Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock

- Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawaga daga jihohin Borno da Yobe a fadarsa da ke Abuja

- Gwamnonin jihohin Borno da Yobe, Farfesa Babagana Zulum da Mai Mala Buni ne suka jagoranci tawagar jihohinsu

- Har wa yau, shugabanin hukumomin tsaro kamar yan sanda, DSS, da wasu ministoci sun hallarci taron

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yanzu yana ganawa da tawaga daga jihohin Borno da Yobe a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni ne suka jagoranci tawagar zuwa fadar shugaban kasar.

Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock
Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock. Hoto: @BayoOmoboriowo
Source: Twitter

Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock
Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock. Hoto: @BayoOmoboriowo
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sheikh Gumi: A wurin tsagerin Niger Delta ƴan bindiga suka koya satar mutane

Sauran wadanda ke cikin tawagar sun hada da tsohon gwamnan Borno Kashim Shettim da Karamin Ministan Noma, Mustapha Shehuri da na Ayyuka da Gidaje, Abubakar Aliyu.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Ministan Ayyukan Jin Kai Sadiya Umar suma sun hallarci taron.

Har ila yau Babban sifetan yan sanda, Mohammed Adamu, NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (mai murabus), da Shugaban hukumar yan sandan farar hula, SSS, Yusuf Bichi suma sun halarci taron.

KU KARANTA: Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

Amma Shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume wanda dan asalin jihar Bonro ne bai halarci taron ba.

Vanguard ta ruwaito cewa taron ba zai rasa nasaba da batun tsaro da gine-gine tsakanin jihohin biyu ba.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel