Bisi Akande ya yi kaca-kaca da sabunta rajistar Jam’iyyar APC da ake yi

Bisi Akande ya yi kaca-kaca da sabunta rajistar Jam’iyyar APC da ake yi

- Cif Bisi Akande ya sabunta rajistarsa a matsayin ‘dan jam’iyyar APC a Osun

- Adebisi Akande ya na ganin cewa wannan aiki zai sa a kashe miliyoyi a banza

- Akande ya gargadi Shugabannin APC na riko da su guji kwadayin dadi-mulki

Tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Cif Adebisi Akande, ya yi suka a game da tsarin da aka kawo na sabunta rajista da zama ‘dan jam’iyya.

Jaridar Daily Trust ta kuma rahoto Adebisi Akande ya na sukar salon Mai Mala Buni wanda ke rike da jam’iyyar a matsayin shugabanta na rikon-kwarya.

Cif Bisi Akande ya yi jawabi ne jim kadan bayan ya yi rajista a gundumarsa ta Isedo1, Ila-Orangun, jihar Osun a ranar Laraba, 3 ga watan Junairu, 2021.

Sanata Lawan Shuaib shi ne wanda ya yi wa tsohon shugaban jam’iyyar rajista a mazabarsa.

KU KARANTA: Bisi Akande da jagororin Yarbawa sun bukaci a duba aikin kwamitin El-Rufai

“Na ji cewa an girmama ni, an karrama ni na cewa jam’iyyar nan ta APC, ta ware ni, ta sake tantance rajistar da na yi a gidan kauye na a lla Orangun.”

An rahoto Akande ya na cewa: “Ku ba ni dama in fadi abubuwa biyu, na farko shi ne a tsarin da aka sani, kwamitin rikon kwarya a jam’iyya bakon abu ne.”

Idan har ba a bi a hankali, an dauki mataki ba, shugabanni masu kauce hanya za su kare da jin kunya.”

“Saboda haka ina kira ga shugabannin rikon kwarya masu-ci, da su guji kwadayin cigaba da zama a mulki, kamar yadda aka saba a kasashe masu tashi.”

KU KARANTA: APC ta na hangen akalla mutum miliyan 2 a Adamawa

Bisi Akande ya yi kaca-kaca da sabunta rajistar Jam’iyyar APC da ake yi
Bisi Akande, jagororin APC da Buhari Hoto: www.dailypost.ng
Source: Twitter

Abu na biyu da Akande ya ce shi ne za ayi barnar kudi ne a banza wajen sake tantance ‘ya ‘yan jam’iyyar, wanda shi ne karo na biyu a kasa da shekara 10.

A cewar Akande a lokacin da aka yi irin wannan aiki a 2014, an batar da fiye da Naira biliyan 1, don haka yake ganin za ayi asarar kudi a lokacin da ake fatara.

Wadanda su ka shaida rajistar Akande sun hada gwamna Adegboyega Oyetola da mataimakinsa, Gboyega Alani; da Timothy Owoeye; sai kuma Diji Ajibola.

Ragowar sun hada da Titilayo Laoye Ponle; Ajibola Basiru, Lere Oriolowo da Gboyega Famodun.

A ranar Juma'ar da ta wuce kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja, ya isa garin Daura inda ya yi rajistar Jam’iyyar APC a mazabarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel