Buni yana maimaita irin kuskuren Oshiomhole - Kungiyar gwamnonin APC

Buni yana maimaita irin kuskuren Oshiomhole - Kungiyar gwamnonin APC

- Salihu Lukman ya zargi Buni da maimaita kura-kuran da tsoffin shugabannin jam'iyya mai mulki suka yi a baya

- Saboda haka ya yi kira ga cewa dole ne a kira taron mambobin jam'iyyar

- Da yake ci gaba da bayani, ya ce dole ne a zabi sabbin shugabanni a babban taron jam'iyyar

Da alama za a ci gaba da samun rikice-rikice a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Wannan ya biyo bayan sanarwar da Darakta-Janar na kungiyar gwamnonin APC, Salihu Lukman yayi.

A cewarsa, shugabancin jam'iyyar na yanzu karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, suna yin irin kuskuren da kwamitin da Oshiomhole ya jagoranta ya yi.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da kawunsa

Buni yana maimaita irin kuskuren Oshiomhole - Kungiyar gwamnonin APC
Buni yana maimaita irin kuskuren Oshiomhole - Kungiyar gwamnonin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Lukman ya ce kwamitin da Adams Oshiomhole ya jagoranta na APC ya gaza kiran taron bangarorin jam'iyyar, lamarin da ke sake faruwa a jam'iyyar karkashin jagorancin Buni na APCCECC.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin mai taken ‘Gwajin Litmus na APC,’ jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce:

“Jarabawa ta farko, saboda haka, imma kwamitin rikon kwarya ta warware kalubalen da ya haifar da rugujewar kwamitin da Kwamrad Oshiomhole ya jagoranta. Ta yaya warware matsalolin da ke fuskantar jam'iyyar ya dace da ka'idojin dimokiradiyya da kyawawan manufofi? "

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun dauki kwakwaran mataki a yayinda fastocin ‘Buhari-Must-Go’ ya bayyana a jihar Arewa

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shekaru bakwai kenan da kafa jam'iyyar APC amma har yanzin ba ta zama haɗaɗɗiyar jam'iyya ba.

Gwamnan ya bayyana jam'iyyar da cuɗuwar jam'iyyun siyasa da suke faman ganin sun zama jam'iyya ɗaya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Ganduje ya yi wannan jawabi ne a wani taro da kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin APC na yankin arewa maso yamma ya shirya a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel