Da Gaske Gwamnatin Tinubu za Ta Rusa NBAIS da Sardauna Ya Kafa wa Musulmai?
- Ma'aikatar ilimi ta kasa ta fito ta yi bayani kan rade-radin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta rusa hukumar NBAIS
- Wani bayani da Sanata Kawu Sumaila ya yi a zauren Majalisar dattawa ne ya jawo yin martani da cewa za a rusa hukumar
- A bayanin da ta yi, ma'aikatar ilimi ta kasa bayyana hakikanin halin da ake ciki tare da karin bayani kan matsayin NBAIS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ma'aikatar ilimi ta kasa ta nuna damuwa kan yadda aka yada cewa gwamnatin Najeriya za ta rusa hukumar NBAIS.
Hukumar NBAIS na da alhakin lura da tsara jarabawa ga dalibai masu nazari a fannin Larabci da ilimin addinin Musulunci a Najeriya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da ma'aikatar ilimi ta yi ne a wani sako da kakakinta,Boriowo Folasade ya wallafa a kafar Facebook.

Kara karanta wannan
An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya
Gwamnati ta karyata batun rusa NBAIS
Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da cewa ta kai ga wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafuka, wanda ke ikirarin cewa gwamnatin Najeriya da majalisar dokoki ta kasa suna duba yiwuwar rusa hukumar NBAIS.
Sanarwar ma'aikatar ilimi ta ce:
"Ma’aikatar na son bayyanawa a sarari cewa wannan ikirari ƙarya ne da aka shirya domin yaudarar jama’a, kuma ba shi da wani tushe."
Game da zuwa m\ajalisar ƙasa kuwa, ma'aikatar ilimi ta ce:
"Domin kauce wa duk wani ruɗani, ma’aikatar ba ta gabatar da wani ƙudiri a gaban majalisar dokoki ta kasa da ke neman soke NBAIS ba, haka kuma ma’aikatar ilimi ta tarayya ba ta gabatar, ƙaddamar, amincewa ko goyon bayan wata manufa da ke da nufin rusa hukumar ko raunana aikinta na doka ba."

Source: Facebook
Ma'aikatar ilmi ta damu da yada jita-jita
Ma’aikatar ta nuna damuwa kan yadda ake yaɗa irin wannan bayanin da ba a tantance ba, wanda ke ƙoƙarin nuna kamar akwai wani yunƙuri daga gwamnati na adawa da NBAIS.
Ta kuma kara da cewa hakan na iya haifar da fargaba, yaɗa bayanan ƙarya da kuma damuwa a tsakanin ɗalibai, iyaye, malamai, ƙungiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki.
Matsayin hukumar NBAIS a Najeriya a yau
Ma'aikatar ilimi ta ce NBAIS na ci gaba da kasancewa hukumar jarabawa da bayar da takardun shaida da aka amince da ita bisa doka, kuma tana aiki a cikin tsarin ilimin Najeriya.
Ta ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da goyon bayan dukkan cibiyoyin ilimi da hukumomin jarabawa da aka kafa bisa doka, bisa tanade-tanaden dokoki da manufofin ilimi na ƙasa, tare da bin ƙa’idojin haɗin kai, adalci da daidaito ga kowa.
Babban sakataren Ma'aikatar ilmi, Boriowa Folasade ya fitar da sanarwar a yammacin Talata.
Legit ta tattauna da Hubu Isa
A wata tattaunawa da wani dalibi da ya yi karatu ya mallaki shaidar karatu ta NBAIS ya bayyana cewa hankalin shi ya tashi da ya fara jin rade-radi game da batun.
Malam Habu ya ce:
"Tunani na fara game da makomar shaidar karatun mu bayan fara jin labarin.
"Yanzu haka akwai wasu yaran mu da suke karatu a makarantun da za su rubuta jarrabawar NBAIS, rusa hukumar zai zama koma baya a gare mu."
Bayanin da Kawu Sumaila ya yi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya yi magana game da hukumar NBAIS a majalisar dattawa.
A maganganun da sanatan ya yi, ya nuna damuwa kan wata buƙata da ministan shari'a ya yi, inda ya mayar masa da martani kan NBAIS.
A bisa abubuwan da Kawu Sumaila ya fada, ya nuna akwai wata damuwa da ke fuskantar NBAIS, inda ya ce bai kamata a samu hakan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

